Shugaba Zelensky Ya Taya Bola Tinubu Murnar Lashe Zabe, Ya Gayyace Shi Zuwa Ukraine
- Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasan Najeriya ya karbi sakon taya murna daga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensyky
- Zelensky ya kuma gayyaci Tinubu zuwa kasar Ukraine da ke Gabashin Turai saboda wasu dalilai
- Idan baku manta ba, Tinubu ya ce zai yi gogayya da Rasha wajen samar da iskar gas ta Turai, akwai tsama tsakanin Ukraine da Rasha
Birnin Kif, kasar Ukraine - Shugaban kasar Ukriane, Volodymyr Zelensky ya aike da sakon taya murnar lashe zabe ga Bola Ahmad Tinubu na Najeriya bayan zaben ranar 25 ga watan Faburairu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kafar yanar gizon kamfen Tinubu/Shettima ta yada a ranar Alhamis 20 Afirilu, 2023.
A cewar sanarwar, Zelensky ya yaba da yadda aka yi zaben Najeriya cikin kwanciyar hankali da lumana, wanda ya kai ga nasarar Tinubu.
Sakon Zelensky ta Tinubu game da zaben 2023
Shugaban na Ukraine, ya kuma bayyana shirin kasarsa na ci gaba da hulda da Najeriya a karkashin jagorancin Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sakonsa na fatan alheri, Zelensky ya mika sakon gayyata ga Tinubu zuwa kasar Ukraine bayan rantsar dashi a ranar 29 ga watan Mayu.
A cewar wani yankin sanarwar ya ce:
“Duba da wannan damar, ina gayyatar da ka kawo ziyarar aiki zuwa Ukraine a duk lokacin da ka samu dama.”
Yiwuwar Tinubu ya ziyarci Ukraine
Shugaban na Ukraine ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa, gwamnati Tinubu za ta mutunta gayyatarsa don kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
Hakazalika, ya ce yana son gwamnatin Tinubu ya shiga a dama da ita a shirin Ukraine na kai hatsi kasashen Afrika don habaka samar da abinci.
Tsawon kwanaki 421 kenan yanzu, kasar Rasha ta kai farmakin mamaya kan al’ummar kasar Ukraine da basu ji basu gani ba, lamarin da ya sa Tinubu yace zai yi gasa da Rasha a fannin makamashi.
Karfin hali: Matashi dan Arewa ya daura damara, zai yi tattaki daga jiharsu don shaida rantsar da Tinubu
Rasha na son wagaza kasata, inji shugaba Zelensky
A wani labarin, kunji yadda shugaban kasar Ukriane ya bayyana shirin Rasha na ci gaba da farmakar kasarsa ba sassautawa.
Ya bayyana cewa, shugaba Putin na Rasha na ci gaba da shirin yadda zai karar da kasarsa ta Ukraine.
Ana ta yaki tsakanin kasashen biyu tun a watan Faburairun shekarar da ta gabata, hakan ya girgiza duniya ta bangarori daban-daban.
Asali: Legit.ng