Sarkin Saudiyya Ya Tuna da Mutanen Jihar Kano Yayin da Aka Soma Azumin Ramadan

Sarkin Saudiyya Ya Tuna da Mutanen Jihar Kano Yayin da Aka Soma Azumin Ramadan

  • Hukumar bada agajin gaggawa a kasar nan, ta raba kayan abincin da cibiyar KSrelief ta aiko
  • An tura shinkafa, wake, man gyada da sauran abinci zuwa ga mutanen Kano da masifa ta same su
  • An yi dace kayan sun iso a daidai lokacin da Musulman Duniya suke dauke da azumi a bakinsu

Kano - Hukumar NEMA mai bada agajin gaggawa a Najeriya, ta soma rabon kayan abincin da kasar Saudiyya ta aiko zuwa ga wasu mutanen jihar Kano.

The Nation ta ce cibiyar nan ta Sarki Salman mai taimakon marasa karfi watau KSrelief ta aiko da gudumuwa ga wadanda ke cikin tsananin bukata.

Shugaban NEMA na kasa, Mustapha Habib ya shaida wannan a karshen makon jiya yayin da aka kaddamar da rabon kayan ga wadanna masifa ta shafa.

Kara karanta wannan

A kalla Rayuka 11 ne Suka Salwanta a Wasu Hadururruka Daban-Daban a Niger

Hajiya Fatima Kassim wanda ta wakilci Mustapha Habib wajen rabon kayan ta ce wannan abin alheri ya zo a daidai, ganin an shiga watan yin azumi.

Fatima Kassim wanda it ace Darektar tsare-tsare da bincike ta ce an raba kayan ne ga mutujm 500 da jarrabawa ta auka masu a Bunkure da wasu garuruwa.

Jaridar ta ce NEMA tayi rabon kayan ne tare da takwararta mai bada agajin gaggawa a Kano ta SEMA.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sarkin Saudiyya
Sarkin Saudi da Shugaban Najeriya Hoto: english.aawsat.com
Asali: UGC

Abubuwan da aka rabawa mutane

Kayan abincin da aka raba a kowane gida sun hada kilo 25 na shinkafa da kilo 25 na wake, kilo 4 na fulawar masa, sannan sai tumaturin leda na kilo biyu.

A cikin wadannan kaya an samu lita biyu na man gyada da gishiri mai nauyin kilo 0.8. A cewar Fatima Kassim, kowane gida ya tashi da kayan kilo 59.8.

Kara karanta wannan

Toh fa: DSS ta hango matsala a Najeriya, ta ba 'yan kasa shawarin kariya

Al'umma ta amfana sosai

Rahoton This Day ya ce hukumomin bada agajin su na sa ran wadannan kaya za su taimaka sosai wajen rage radadin da wadannan mutane suka shiga ciki.

Da yake jawabi a wajen rabon, jami’in Jakadancin Saudiyya a Kano, Nawaf Muhammad ya yabawa cibiyar da Sarkin Saudiyya kan wannan alheri.

Wani Abdulaziz Muhammad ne ya yi jawabi a madadin sauran wadanda suka amfana da kayan abincin, yana mai kira irin wannan tsari ya dore a haka.

Tinubu ya soke biki a bana

Babu bidiri ko sharholiyar da za ayi yayin da ranar haihuwar Bola Tinubu ta zagayo a yau. Rahoto ya zo cewa za ayi amfani da ranar ne a wajen yin addu’o’i.

Malamai za su yi addu’o’i da karatun kur’ani da hudubobi da nufin Tinubu wanda yanzu haka yake Umrah a kasar Saudi Arabiya ya samu sa'a a mulki.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng