2023: An Kai Karar Hadimin Tinubu a Babban Kotun Duniya Saboda Bakaken Kalamai
- Farfesa Gideon Christian ya yi nasarar aikawa kotun ICC korafi na musamman a kan Bayo Onanuga
- Ana tuhumar Bayo Onanuga da yin kalaman da za sui ya jawo rikicin zabe da yakin kabilanci
- A madadin ICC, Mark P. Dillon ya tabbatar da takardar karar ta shiga hannunsu, za a dauki mataki
Hague - A ranar Litinin aka tabbatar da cewa babban kotun Duniya watau ICC ya karbi karar da aka shigar a kan Bayo Onanuga a kan zaben Najeriya.
This Day ta ce Bayo Onanuga shi ne Darektan yada labarai a kwamitin yakin zaben Bola Tinubu wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Jam’iyyar APC.
Farfesa Gideon Christian ya aikawa ICC da korafi domin ta binciki Bayo Onanuga bisa zargin jawo rikicin zabe da kuma kokarin haddasa fadan kabilanci.
Kotun ICC ya tabbatar da cewa ya karbi wannan korafi mai lamba OTP-CR-109/23 a ranar 27 ga watan Maris 2023, hakan ya nuna za a iya duba lamarin.
Mark P. Dillon ya sa hannu
Kamar yadda rahoton ya zo mana, shugaban sashen yada labarai da bangaren hujjoji na ofishin binciken ICC, Mark P. Dillon ya sa hannu a takardar nan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Takardar Dillon ta ce: “Ofishin Mai gurfanarwa na babban kotun Duniya ya karbi takarda ko wasikarku.
An shigar da wannan takarda a rajistar ofishin nan. Za mu duba takardar kamar yadda ya kamata, bisa la’akari da tsarin aikin babban kotun Duniya."
A sani cewa karbar wannan takarda bai nufin an soma gudanar da bincike a kai ko kuwa za a fara bincike a karkashin Ofishin Mai gurfanarwa a ICC.
Zaben 2023: "Abin Da Yan Adawa Suka Shirya Yi Yayin Rantsar Da Ni", Tinubu Ya Yi Fallasa, Ya Ambaci Sunaye
Da zarar an fara (bincike), za mu sanar da ku a rubuce dauke da dalilan matakin da aka dauka."
- Mark P. Dillon
Bukatar Farfesa Gideon Christian
A takardar da ya aikawa kotun, Farfesa Christian ya roki ayi bincike a kan abubuwan da suka rika fitowa daga shafin Onanuga a zaben da aka yi a Najeriya.
Ana zargin Hadimin ‘dan takaran shugaban kasar da yi wa kabilar Ibo barazana a Twitter, wanda irin haka ya jawo kashe-kashe a Ruwanda da Burundi.
PDP ta ce za ayi mata magudi
A rahoton da muka fitar a baya, an ji PDP ta ce ta samu hujja da take nuna Kwamisinan INEC yana tare da jam’iyyar APC a zaben Adamawa.
Debo Ologunagba ya ce tun farko an so dauke aikin tattara zaben Adamawa daga Yola zuwa Abuja, ya ce ji APC ta na tunkaho da sai yadda tayi da INEC.
Asali: Legit.ng