Dangote Ya Samu Naira Biliyan 460 a Cikin Kwana 1, Ya Zama Attajiri na 83 a Duniya
- Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya samu kudin da sun kai Naira Biliyan 460 a cikin sa’a 24
- Simintin Dangote yana cigaba da kasuwa, hakan ya ba Alhaji Aliko Dangote fam Dala miliyan 100
- A Duniyar yau, arzikin Attajirin kasar Najeriyan ya fi na Alexey Mordashov da Alisher Usmanov
Abuja - Mai kudin Najeriya da Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya mallaki Naira Biliyan 460 a cikin kwana daya a kwana-kwanan bayan nan.
Bayanin da aka samu daga Bloomberg Billionaire Index ya nuna makudan kudin da Aliko Dangote ya samu, ya sa ya motsa a jerin Attajirai.
Shekaru 12 kenan a jere har yanzu babu wanda ya sha gaban Dangote ta fannin arziki a nahiyar Afrika, yanzu ya mallaki Dala Biliyan 19.7.
Rahoton ya ce arzikin ‘dan kasuwan ya karu ne a sanadiyyar yawan bukatar simintin Dangote da ake yi, hakan ya kara masa $100m.
Simintin Dangote ya yi daraja
Simintin Dangote ya cigaba da daraja a kasuwa, ana saida hannun jarinsa daya a kan N288. Alkaluman NSE na kasa ya tabbatar da haka.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Baya ga Dalolin miliyoyin da ya samu, bakanon ya gwabje Attajirai hudu da suke gabansa a da. Za a samu wannan rahoto a jaridar Punch.
Kamar yadda Legit.ng Hausa ta lura, yanzu Dangote ya zarce Alexey Mordashov da Alisher Usmanov wanda fitattun masu kudi ne a Rasha.
Da farko sai da Alhaji Dangote ya zama na 81 a masu kudin Duniya gaba daya, amma a makon da ya gabata ya yi asarar kusan Naira Biliyan 13.
A rahoton da muka samu daga Sun, duk da haka Dangote yana gaban takwarorinsa, Chuan-Fu da Lakshmi Mittal da ke kasashen Sin da Indiya.
Masu kudin Duniya
A sahun attajiran farko na Duniya, an sha gaban Elon Musk, har yanzu kuma ana damawa da Bill Gates. Ga yadda lissafin yake zuwa yau:
1. Bernard Arnault
2. Elon Musk
3. Jeff Bezos
4. Bill Gates
5. Warren Buffett
Karin albashi a Legas
Rahoto ya zo cewa kowane ma'aikacin Gwamnati zai samu karin 20% a kan albashin da ya saba karba a Legas daga wannan watan na Maris.
Babajide Sanwo-Olu ya waiwayi ma’aikata, masu aiki a kananan hukumomi da malaman makaranta kamar yadda gwamnati ta sanar.
Asali: Legit.ng