Dan Kwallon Najeriya Ya Yanke Jiki Ya Fadi Matacce Yayin Buga Wa Kungiyarsa Wasa A Turai
- Hadi Bala Ado, dan kwallon Najeriya da ke buga wa kungiyar CD Madridejo wasa a kasar Spain ya rasu
- Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya yanke jiki ya fadi ne yayin da ake tsakiyar wasa a ranar Lahadi
- Misbau Ado Bala, yayan marigayin ya tabbatar da rasuwar kaninsa da ya ce babban rashi ne ga duniyar kwallo, Najeriya da iyalansu
Spain - Tsohon dan kwallon kungiyar Jigawa United, Hadi Bala Ado, ya yanke jiki ya fari yayin da ake wasa tsakanin kungiyarsa, CD Madridejo FC da SP Cabanillas a matakin ta biyu na Spain Terceira.
An rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 5 ga watan Janairun shekarar 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar kwallon kafa na The Castilla-La Mancha cikin wata sanarwa ta da ta fitar ta ce matashin dan kwallon na Najeriya ya yanke jiki ya fadi ba tare da wani matsala na zahiri ba cikin minti 39 na wasan.
Rahotanni sun bayyana cewa tawagar ma'aikatan lafiya da ke filin wasan Municipal Toledo sun garzaya don kai masa dauki, amma duk kokarin da suka yi na farfado da shi bai yi nasara ba.
Yayan Hadi ya tabbatar da rasuwarsa
Da ya ke magana da Daily Trust a Kafanchan, jihar Kaduna yayan marigayin, Misbau Ado Bala, wanda ya yi magana a madadin iyalan ya bayyana mutuwa a matsayin babban rashi ga Najeriya da duniyar kwallo da kuma yan uwan mamacin.
Kungiyoyin kwallon kafa da Hadi ya yi wa wasa a baya
Dan kwallon dan shekara 21, haifafan garin Kafanchan, Hadi, ya fara wasan kwallo ne da kungiyar Arewa United da wasu kungiyoyi kamar Shareef Academy, Golden Balley, Zaria Bees da Salama FC duk a Kafanchan kafin ya tafi jihar Plateau sannan Jigawa.
Dan kwallon Najeriya ya yanke jiki ya fadi ya mutu lokacin da ake buga kwallo a Legas
A wani labari mai kama da wannan, kun ji cewa wani matashin dan kwallon kafa dan shekara 31 ya yanki jiki ya fadi matacce yayin da ake tsakar buga wasa a Lekki, jihar Legas.
An tattaro cewa matashin dan wasan wanda ba a bayyana sunansa ba yana kokarin bin kwallon ne a lokacin da ya yanke jiki ya fadi.
A cewar rahotanni, marigayin dan wasan bai samu dauki cikin gaggawa ba domin sauran abokan wasansa na kwallo suna zargin yana kokarin daidaita numfashinsa ne.
Asali: Legit.ng