Na Yi Nadamar Zana Tattoo Din Messi a Goshi Na, Bata Kawo Min Alheri Ba, In Ji Jambs

Na Yi Nadamar Zana Tattoo Din Messi a Goshi Na, Bata Kawo Min Alheri Ba, In Ji Jambs

  • Mike Jambs, wani mai karfin fada a ji a soshiyal midiya ya ce ya yi nadamar zana tattoo din Lionel Messi a goshinsa
  • Jambs yana daga cikin dimbin masoya Messi da tawagar kwallon kafa na Argentina da suka rika yin tattoo din kofin duniya ko Messi bayan nasarar
  • Da farko dai Jambs ya nuna cewa shi bai aikata laifi ba sai daga baya ya yi mi'ara koma baya ya ce ya yi nadamar yin tattoo din don ba alheri ta kawo masa ba

Columbia - Wani mai karfin fada a ji a soshiyal midiya, Mike Jambs, wanda ya rubuta sunan Lionel Messi a fuskarsa bayan nasarar da Argentina ta yi na cin kofin duniya ya ce ya yi nadamar hakan.

Masoyin ya rubuta kalmar 'MESSI' a goshinsa da taurari uku a kumatunsa da ke nuni da kofin duniya uku da Argentina ta ci tun fara gasar cin kofin duniya, Daily Mail reported.

Kara karanta wannan

Bidiyon Matar Aure Tana Gaggawar Ba Miji Abinci a Baki Kada ya Makara Aiki ya Janyo Cece-kuce

Mike Jambs
Na Yi Nadamar Zana Tattoo Din Messi a Goshi Na, In Ji Jambs. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A shafinsa na Instagram, Jambs tunda farko ya kare kansa kan matakin da ya dauka a lokacin da ya wallafa bidiyon kansa ana zana masa tattoo din.

Ya ce:

"Ban yi wa kowa rauni ba, ban kuma aikata abin da ya saba doka ba."

Matsala kawai tattoo din na Messi ta rika janyo min da yan uwa na - Jambs

Amma, daga baya, Jambs ya yi mi'ara koma baya, inda ya ce dama a ce zai iya warware abin da ya yi.

Ya koka da cewa:

"Na yi nadamar yin tatto din, a maimakon kawo min abin alheri, sai abu mara kyau ya kawo min tare da iyali na."

The Punch ta rahoto cewa masoya kungiyar kwallon kafar ta Argentina sun yi layyi a Buenos Aires don a yi musu tatto din Messi da kofin duniyan.

Kara karanta wannan

Yaro Man Kaza: Bidiyon Karamar Yarinya Tana Sharar Bacci a Tsaye Ya Bar Mutane Baki Bude

Mai yin tattoo, Esteban Vucinovich ya fada wa AFP a babban birnin kasar cewa:

"Nan da sati biyu, mutane sun biya kudi zan musu tattoo masu alaka da kofin duniya."
"Wasu a baya da suke son a musu tattoo na maciji ko kokon kai sun canja zuwa na Messi ko kofin duniya. Ina yi wa mutum biyu zuwa uku a kullum."

Mafi yawancin tattoo din na kofin duniyan ne, in ji Vucinovich, sai Messi da kuma mai tsaron gida, Emiliano Martinez wanda ya taka muhimmin rawa don nasarar Albiceleste a wasar ta na karshe da Faransa.

Mahaifiyar Pele ba ta san danta ya rasu ba, In Ji yar uwarsa

Yar uwar, marigayi Pele, Maria Lucia do Nascimento ta ce har yanzu mafiyarsu ba ta san fitaccen dan kwallon duniyan ya mutu ba.

A hirar da ta yi da Mirror UK, Maria Lucia ta bayyana cewa mahaifiyarsu wacce ta haura shekaru 100 ba ta cika fahimtar abubuwan da ke faruwa a yanzu ba.

Kara karanta wannan

Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164