‘Yan Majalisar Dattawa Sun Zage Tare da Ba Hammata Iska Ana Tsaka da Zama a Zauren

‘Yan Majalisar Dattawa Sun Zage Tare da Ba Hammata Iska Ana Tsaka da Zama a Zauren

  • Yan majalisa sun zage tare da bai wa hammata iska inda suka dinga naushin juna tare da bugawa juna kujerun zauren majalisa
  • Lamarin nan ya faru ne a ranar Laraba a majalisar tarayyar kasar Sierra Leone bayan gabatar da bukatar sauya dokokin zabe da jam’iyya mai mulki tayi
  • Ta kai ga sai da kakakin majalisar dattawa ya kira ‘yan sanda wadanda suka tsaya yayin da ake zaman sannan suka dinga jefa wasu ‘yan majalisar waje

‘Yan majalisa sun ba hammata iska a ranar Laraba yayin da aka yi zama kan batun sauya tsarin zaben kasar wanda zai bada damar wakilci daidai da daidai a zaben shekara mai zuwa a kasar Sierra Leone, jaridun kasar suka rahoto.

Taswirar kasar Sierra Leone
‘Yan Majalisar Dattawa Sun Zage Tare da Ba Hammata Iska Ana Tsaka da Zama a Zauren. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

A bidiyon da ya bayyana, ‘yan majalisar wakilai daga jam’iyyar Sierra Leone People’s Party mai mulki da na jam’iyyar adawa ta All People’s Congress an gansu suna musayar naushi tare da jifa da kujeru.

Kara karanta wannan

Shugabbanin Kudu Sun Koka Kan Yadda Aka Maida su saniyar Ware Musamman A Faggen Shugabancin

A wani wuri kuwa, wani abu da yayi kama da katuwar tulu fulawa ce aka wurga a zauren majalisar, Channels TV ta rahoto.

Hukumar zaben kasar Afrika ta yamman ta bukaci sauya tsarin zaben kasar da za a yi a watan Yunin 2023 da kuma majalisar kasar wanda za a yi rana daya, lamarin da jam’iyyar adawa ta kushe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnatin kasar ta amince da shirin amma kuma akwai bukatar ‘yan majalisar kasar su amince.

Dole ta sa aka kira ‘yan sanda

Eye Radio ta rahoto cewa, Matthews Sahr Nyuma, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, ya tabbatar da aukuwar damben a zauren majalisar.

“Doka ce ta bada damar hukumar ta daidaita lamurran zabe kuma abokan aikinmu sun ki bin yadda majalisar ta tanadar shine suka yanke hukuncin yin wannan abu.”

Kara karanta wannan

Gara in Mutu da dai in Gazawa Magoya Bayana, Peter Obi

- Yace.

“Kakakin majalisar bashi da yadda zai yi. Dole ta sa aka kira ‘yan sanda domin cigaba da abinda ya kawo mu majalisar.”

Bayan bai wa hammata iskar wanda ya fara wurin karfe 11 na agogon GMT kuma aka kammala zuwa rana, wasu daga cikin ‘yan majalisar dole tasa jami’an tsaro suka wurga su waje, wani ‘dan jarida ya sanar da AFP.

A zaben watan Yunin da za a yi, Shugaba Julius Bio wanda ya hau karagar mulkin kasa a 2018 zai sake takara kashi na biyu don zarcewa.

An yi dokar daidaiton jinsi a makon da ya gabata

A makon da ya gabata, ‘yan majalisar sun saka dokar gabatar da wani kaso na mata a dukkan zabuka da mukamai kafin zaben shekara mai zuwa wanda ya zama babban alkwarin da shugaban kasa ya dauka a 2018.

Sierra Leone kasa ce dake da mutane kusan miliyan takwas kuma suna da zaman lafiya a tarihi tun bayan yakin basasa da aka yi tsakanin 1991 zuwa 2002 wanda yayi ajalin mutum 120,000.

Kara karanta wannan

Mun tuba: PDP ta tafka kura-kurai daga 1999 zuwa 2015, Atiku zai gyara komai

Yan majalisa sun sha dambe kan rabon fatanya

Legit.ng ta rahoto yadda ‘yan majalisar kasar Uganda suka sha dambe kan rabon fatanya da aka yi.

Daya daga cikin ‘yan majalisar ce ta fara tado zancen kan batun wasu daga ciki basu samu fatanyar da aka raba ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng