'Yan majalisa sun bawa hammata iska a kan rabon fatanya

'Yan majalisa sun bawa hammata iska a kan rabon fatanya

Taron majalisa na ranar Talata a Uganda ya tashi babu dadi a kan rashin jituwar da ta ratsa tsakanin 'yan majalisar a kan kason fatanya da gwamnatin za ta yi.

A yayin bayyana a gaban kwamitin kasafin don gabatar da rahoto a kan bangaren aikin gona, Janet Grace Okori-moe ce shugaban kwamitin majalisar wacce alhakin siyo fatanyar ke kanta. Hakazalika, sai zababbun 'yan majalisar ne aka ware don basu fatanyu da zasu raba wa mazabarsu.

'Yar majalisar mai suna Cecilia Ogwal ce ta fara tada zancen fatanyun saboda da yawa daga cikin 'yan majalisun basu samu ba, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda Ogwal ta ce, a shekaru biyu da suka gabata ne a ka bada fatanyu dari-dari. Ta zargi cewa an zabi wasu 'yan majalisun an basu ne tare da wasu ministoci wadanda ke da kusanci da gwamnati. Ta ce yankuna da yawa a Dokolo ba su samu fatanyun ba.

"Mun fitar da kudi don siyen fatanyu amma shiru kake ji. Mun samu labarin cewa kowanne minista ya samu fatanyu 25,000 sannan wasu tsirarun 'yan majalisar sun samu," in ji ta.

DUBA WANNAN: Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

Amma kuma, Solomon Silwanyj dan majalisar Bukooli ta tsakiya kuma kwamishina ya musantan zargin. Ya bukaci shugabar kwamitin da ta soke zargin Ogwal ganin cewa an raba fatanyun yadda ya dace.

"Ogwal ta dago wani zargi a kwamitin nan wanda bai dace ba, mara tushe kuma mai rikitarwa," ya ce.

Amma kuma kwamitin ba su kammala maganar fatanyu ba saboda sun saka wata rana don haduwa da masu ruwa tsaki.

Duk kokarin tuntubar ministan aikin noma Vincent Ssempijja don tsokaci a kan lamarin bai yuwu ba.

A yakin neman zaben shugaban kasa Yoweri Museveni a 2016, ya yi alkawarin wadata kowanne gida da fatanya don ci gaban noma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel