Cin Hanci: Kotun Sin Ta Yankewa Jami’in Gwamnati Hukuncin Kisa Duk da Ya Tuba

Cin Hanci: Kotun Sin Ta Yankewa Jami’in Gwamnati Hukuncin Kisa Duk da Ya Tuba

  • Liu Guoqiang ya gamu da hukuncin kisa da kuma daurin shekaru biyu a kurkuku saboda karbar cin hanci
  • Mista Guoqiang ya kasance babban mai bada shawara kan harkokin siyasa a lardin Liaoning a kasar Sin
  • Shi da kan shi ya amsa laifinsa, don haka Alkalin kotun ya yi masa rangwame a hukuncin da ya zartar

China - Wata kotu da ke kasar Sin, ta yanke hukuncin kisa da dauri na tsawon shekaru biyu ga Liu Guoqiang saboda laifin karbar cin hanci.

Hukumar dillacin labarai da ta dauko labarin, tace Liu Guoqiang ya taba rike kujerar Mai bada shawara a kan harkokin siyasa a shiyyar Liaoning.

Jaridar China Daily a rahotonta, tace wata kotu da ke garin Tianjin ta samu ‘dan siyasar da laifin karbar cin hancin $48m (fam 352 million yuan).

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Guoqiang ya taba zama mataimakin shugaban kwamitin Liaoning na kungiyar siyasar nan ta Chinese People’s Political Consultative Conference.

Cin hanci a Liaoning

Kamar yadda jawabin da kotu ta fitar a ranar Talatar ya nuna, ‘dan siyasar ya yi wannan aikin ashha ne a lokacin da ya yi aiki a garin Liaoning.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsakanin 2006 da 2016 da yake ofis, tsohon matimakin gwamnan ya yi amfani da damar da ya samu wajen samun tarin dukiya da karin matsayi.

Kasar Sin
Kotu a kasar Sin Hoto: www.chinadaily.com
Asali: UGC

Kotu tace wanda aka yi kara ya amsa laifinsa da kansa, yace ya karbi cin hanci da nufin Mai shari'a ya yi masa sassauci a wajen hukuncin na sa.

Da ya tashi bayani, Guoqiang ya tono har da laifuffukan da hukuma ba ta san da su ba.

Liu Guoqiang ya rasa komai a kotu

A karshe an karbe dukiyar da ya karba kuma aka maida ta Baitul-mali, aka dauke duk kadarorinsa, sannan aka hana shi shiga harkar siyasa.

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

21st Century Chronicle tace bayan ya shekara biyu a gidan maza, za a iya maida hukuncin kisan da aka yi masa ya zaman a daurin rai da rai.

Karin albashi a Najeriya

An ji labari Hukumar RMAFC mai yanke albashin ma’aikata da ‘yan siyasa a kasar nan ta fadi wadanda suke tashi da makudan kudi a Najeriya.

Mr. Mohammed Shehu yace duk da miliyoyin kudin da ake biyan Muhammadu Buhari a duk wata, wasu jami’an gwamnati sun sha gaban shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel