Taliban Za Ta Haramta Amfani Da TikTok Saboda Yana 'Asassa Tashin Hankali'

Taliban Za Ta Haramta Amfani Da TikTok Saboda Yana 'Asassa Tashin Hankali'

  • Taliban mai mulkin kasar Afghanistan ta sanar da cewa tana daf da haramta amfani da TikTok a kasar
  • A cewar ma'aikatar sadarwa na Taliban, TikTok na asassa tashin hankali da gurbata tarbiyyar matasan kasar
  • Taliban ta ce dandalin na TikTok na wani wasan bidiyo na PUGB suna koyar da dabi'un mutanen yamma wanda ya ci karo da tsarin musulunci na kasar

Afghanistan - Taliban ta sanar da cewa za ta haramta amfani da dandalin sada zumunta na TikTok saboda yana karfafa tashin hankali, LIB ta rahoto.

Ma'aikatar Sadarwa ta Taliban ta ce shahararren manhajar da PUBG, wani wasan bidiyo da ake yi a intanet duk za a haramta su a kasar cikin yan makonni.

Taliban
Taliban Za Ta Haramta Amfani Da TikTok Saboda Yana 'Asassa Tashin Hankali'. Hoto: @daily_trust.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Zan Iya Dukan Kirji In Rantse Cewa Mijina Bai Taba Cin Amanata ba, Jarumar Fim

Wani jami'in Taliban ya shaidawa Mail Online cewa:

"TikTok na yadda badala da abubuwan da bidiyo da musulunci bai yarda da su ba tsakanin matasan Afghanistan, kuma dole mu hana abin saboda goben matasan mu ya yi kyau."
"Suna lalata mana tarbiyan matasa ta hanyar tallata tsarin rayuwan mutanen yamma. A kasar musulunci muke zaune kuma wadannan shafukan na watsa abubuwan da suka ci karo da shi."

Jami'in ya kara da cewa:

"Shima Facebook yana yadda wasu daga cikin irin wannan abubuwan. Matasan mu na bata lokaci sosai saboda shi. Hakkin mu ne mu kula da matasa."

Za a hana mutane iya amfani da wadannan fitatttun manhajojin a kasar.

Sabbin shugabannin na Afghanistan sun sanar da wannan matakin ne a wani taro da wakilan sashi tsaro da hukumar aiwatar da shari'a.

Hakan na zuwa ne bayan haramta wakoki, fina-finai da wasannin kwaikwayo na talabijin inda aka ga taliban na lalata kayan kide-kide.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta haramtawa 'yan Najeriya cin gandan fatar dabbobi, ta fadi dalilai

Taliban ta haramta wa wanzamai aske wa mutane gemu, ta hana sauraron waƙoƙi a Afghanistan

A wani rahoton, kun ji cewa an haramta wa wanzamai a yankin Helmand aske wa mutane gemunsu da saka wakoki a rediyo ko talabijin a shagunan aski, Daily Trust ta ruwaito

A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Lahadi, sashin habbaka tarbiya da kare aikata masha'a na yankin ya umurci wanzamai da masu askin zamani su yi biyayya ga sabon umurnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel