Bidiyon Yadda Biri Ya Kwace Wayar Salular Wata Mata Kuma Ya La'anta Shi A Gabanta

Bidiyon Yadda Biri Ya Kwace Wayar Salular Wata Mata Kuma Ya La'anta Shi A Gabanta

  • Wani biri da ke gidan zoo a kasar Burundi ya bawa wata mata mamaki a yayin da ya fizge wayanta na salula bayan ta kusanci kejinsa
  • Birin ya ki mayarwa matar wayanta sai ma ya rika goga wayar da karfi a jikin karfen kejinsa hakan yasa wayar ta lalace sosai
  • Daga bisani ma'aikatan gidan zoo din sun yi nasarar karbo wayan daga hannun birin sannan matar ta karbi wayar ta kama hanya ta tafi

Burundi - Wata mata wacce ta kusanci wani biri a gidan zoo ta gamu da abin da daga mata hankali bayan dabbar ya kwace wayarta kuma ya ki mayar mata.

Matar wacce ta ziyarci gidan ajiye dabobin ta yi sakaci ne kuma birin ya maza ya kwace wayar da ke hannunta.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sa Koma Makarantar Da Nayi Digiri Nace Su Dawo Min Da Kudi Na

Biri a gidan Zoo
Bidiyon Yadda Biri Ya Kwace Wayar Salular Wata Mata Kuma Ya La'anta Shi A Gabanta. Hoto: @lindaikeji.
Asali: Twitter

Daga nan birin ya rika goga wayar a jikin karafunan da ke zagaye da dakinsa yana daka tsalle kamar yadda bidiyon ya nuna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A lokacin da ma'aikatan zoo din suka iso kuma suka karbo wayan daga hannun birin, ya riga ya yi wa wayar babban ila.

An mayar wa matan wayar a lalace kuma ta kama hanya ta tafi tare da wani namiji da suka taho tare.

Ga bidiyon yadda abin ya faru:

Martanin wasu masu amfani da intanet

Gej Mgbenka Ifeanyi OkijaAmaka:

"Duk cikin rayuwa ne da darrusa."

Nwachukwu Patrick:

"Shin wannan Zoo ne ko dai dauri."

UkoJemima Pukuma:

"Wane irin sakaran biri ne wannan."

Edidiong Inyene:

"A lokacin da ka yi kokarin wuce gona da iri."

Bright Agujioke:

"Birin da ya yi kwana uku bai ci abinci ba kina son daukan selfie da shi, ki gode wa Allah bai miki illa ba.

Kara karanta wannan

Hotunan Ummi, Kyakkyawar Budurwar Da Ta Rasa Ranta A Farmakin Da Yan Bindiga Suka Kai Bankunan Kogi

Onyejiuwa Chukwuemeka:

"Kun tabbata wannan biri ne kuwa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel