Elizabeth II: Za a Kashe Kusan Naira Biliyan 4 Wajen Bikin Jana’izar Sarauniyar Ingila
- Mutuwar Sarauniya Elizabeth II zai jawo kasa Birtaniya ta $6.9b wajen jana’iza da nadin sabon Sarki
- A makon da ya wuce aka ji Elizabeth II ta rasu tana shekaru kusan 100, ta shafe shekaru 70 a mulki
- Gwamnati tana cikin matsin tattalin arziki, amma haka nan za a batar da kudi wajen bikin jana’iza
United Kingdom - Gwamnatin Birtaniya tana shirin kashe makudan kudi domin jana’izar Marigayiya Elizabeth II wanda ta mutu a makon jiya.
AJ Plus ta bi diddikin shirye-shiryen da ake yi domin birne Sarauniyar Ingila watau Elizabeth II, jaridar tace gwamnati ta ware har Dala miliyan 9.
Hakan yana nufin abin da za a batar domin birne Sarauniyar ya kai N3.85bn a kudin Najeriya.
Za ayi wannan a lokacin da tattalin arzikin kasar Birtaniya yake neman tsukewa, kuma akwai sama da mutane miliyan biyu da ke neman abinci.
Facaka ko karrama masarauta?
Rahoton AJ + a Twitter ya nuna yanzu haka ana fama da tsadar rayuwa a Birtaniya, amma ana shirin batar da makudan kudi a jana’izar Elizabeth II.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hasashen da aka yi, ya nuna kusan 14% na manyan mutanen da ke rayuwa a Ingila ba su iya cin abinci sau uku a rana saboda yadda kaya suka tashi.
Kudin abincin yara miliyan uku a makabarta
Akwai yara 800, 000 da iyayensu ba su da hali da ba su samun abinci a makarantu. $2.85 ake warewa kowane yaro, $9m zai ciyar da yara miliyan 3.15.
Baya ga yunwa da ke damun 33% na yara a kasar Turan, makarantu da-dama suna rage abincin da suke rabawa dalibansu a dalilin tsadar kayan abinci.
The Guardian tace nan da ‘yan watanni za a ji farashin mai da gas ya tashi da 27% a Ingila.
Sannan anyi hasashen mutum 1.3 za su shiga cikin kungurmin talauci a bana, adadin marasa hali zai zarce miliyan 15.2, a karon farko tun shekarar 2000.
Rahoton List ya koka cewa asibitoci sun fasa ganin marasa lafiya a ranar 19 ga watan Satumba saboda hukuma ta bada hutu domin a birne Sarauniya.
Sabon Sarki ya hau mulki
A baya mun kawo maku rahoto na takaitaccen bayani game da Charles Philip Arthur George watau Sarki Charles na III wanda ya zama Sarkin Birtaniya.
An haifi Charles na III a 1948, sabon Sarkin ya zama mai jiran gadon sarauta tun yana shekara uku rak da haihuwa, sai bayan shekaru 70 ya dace.
Asali: Legit.ng