Sarauniya Elizabeth Ta II: Abubuwa 5 Da Za Su Faru Yanzu Bayan Mutuwar Sarauniyar Mafi Dadewa Kan Mulki
- A yayin da duniya ke yi wa sarauniya addu'ar samun sauki, wasu da dama suna tunanin mai zai faru idan abin da ba a fata ya kasance
- Tunda farko, mutane da dama sun bayyana cewa sanarwar da fadar Buckingham ta fitar kan rashin lafiyar sarauniyar ya nuna abin ya yi tsanani
- Legit.ng ta yi bincike kan abubuwan da za su faru yanzu da sarauniya Elizabeth ta II ya riga mu gidan gaskiya
Kafin sanarwar rasuwarta, mutane a fadin duniya sun shiga yanayin damuwa bayan da fadar Buckingham ta sanar cewa likitoci na duba Sarauniya Elizabeth ta II a Scotland.
Wasu da dama kuma sun ce sanarwar da fadar gidan sarauntan na Birtaniya ya fitar, wacce ya ce likitoci sun damu da halin da ta ke ciki ya nuna rashin lafiyar ya yi tsanani.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Amma, Fadar ta Buckingham ta sanar cewa Sarauniyar ta rasu cikin salama a barcinta a ranar Alhamis a Balmoral, a gidan sarauta a Scotland.
Mene Zai Faru Idan Sarauniya Ta Rasu?
Legit.ng ta yi bincike kan abin da zai faru yanzu da sarauniyar ta rasu.
Abubuwan da za su faru bayan rasuwar sarauniyar suna cikin wani tsare-tsare da fadar ta yi mai suna "Operation London Bridge."
Za a aiwatar da tsare-tsare da zarar sarauniyar ta rasu.
1. Sanar da rasuwar ta hanyar amfani da wani yare na musamman
Idan Sarauniya Elizabeth na II ta rasu, za a sanar da rasuwarta tsakanin manyan jami'an gwamnati ta hanyar amfani da yare na musamman "London Bridge is down".
Farai ministan Birtaniya, sakatare da wasu manyan jami'an gwamnati za su samu wannan sakon daga fadar Buckingham.
Daga nan za a watsa labarin zuwa kasashen duniya da suke mambobin kungiyar hadin kan kasashen rainon Birtaniya.
Daga bisani, za a sanar da labarin a kafar watsa labarai ta Birtaniya wato BBC.
2. Bakaken hotuna a shafukan sada zumunta
Bayan hakan fadar za ta fara nuna launin alhini a dukkan shafukanta na dandalin sada zumunta, musamman launin baki. Kuma, za a fitar da sanarwar rasuwar a hukumance a dukkan shafukan intanet sannan za a saka sanarwar a kofofin shiga fadar Buckingham.
3. Za a sanar da sabon sarki
Yarima Charles - babban dan saruaniyar - zai yi jawabi ga duniya kuma za a sanar da shi a matsayin sabon sarkin Birtaniya.
4. Zaman makoki na kwana 11
Za a yi zaman makoki irin na manyan mutane a ranar rasuwar da kwana 10 a Westminster Abbey, sannan za a shafe mintuna biyu tsit babu cewa komai misalin karfe 12 na rana a kasar baki daya.
Kazalika, za a yi zaman makoki a fadar gidan sarauta a Landon da Windsor. Za kuma a yi wani zaman makokin a cocin St George da ke Windsor.
5. Birne marigayiyar Sarauniyar a Windsor
Daga nan kuma za a birne sarauniyar a cocin tunawa da Sarki Goerge VI da ke Windsor.
Asali: Legit.ng