Tarihin Sarki Charles III, Wanda Ya yi Shekaru 70 Yana Jiran Gadon Sarauta

Tarihin Sarki Charles III, Wanda Ya yi Shekaru 70 Yana Jiran Gadon Sarauta

  • London – Babban ‘dan Queen Elizabeth II da Prince Philip ya dare karagar gidan sarautar Birtaniya
  • Sarki Charles III ya gaji mahafiyarsa wanda ta rasu bayan tayi shekaru 70 tana kan mulki a kasar Ingila
  • A lokacin da kakansa (George VI) ya rasu, Sarkin yana da shekaru uku a Duniya, uwarsa ta karbi sarauta

Mun kawo takaitaccen bayani game da Charles Philip Arthur George watau Sarki Charles na III wanda ya zama Sarkin Birtaniya:

1. CBC News sun rahoto cewa an haifi Sarki Charles na III ne a Nuwamban 1948, shekaransa 73.

2. Sabon Sarkin ya zama mai jiran gadon sarauta tun yana shekara uku rak da haihuwa.

3. Charles III ne na farko a cikin masu jiran gado da yana nan mahafiyarsa ta dare kan karaga.

Kara karanta wannan

Taikaitattun bayanai masu kayatarwa da ya kamata ku sani game da sarauniyar Ingila Elizabeth

4. Sarkin ya yi karatu ne a makaranta tare da sauran yara a maimakon a koya masa a gida.

5. Mai martaba yana da Digiri da Digirgir a fannin fasaha daga jami’ar Cambridge.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

6. ABC tace Marigayiya Elizabeth II ta nada shi ya zama Yariman Wales tun shekarar 1969.

7. Baya ga sarauta, Sarkin ya yi aikin sojan ruwa da na sama kamar mahaifinsa, George VI.

Auren Diana da Charles III

8. Kusan auren dole aka yi masa da Diana, saboda yace mahaifinsa yana son su tare.

Sarki Charles III
Sabon Sarki Charles III Hoto: NY Times
Asali: UGC

9. A shekarar 1992 ma’auratan suka yarda za su rabu, sai 1996 suka raba jiha.

10. Diana ta mutu a 1997 a wani hadarin mota da ya kashe har da saurayinta, Dodi Fayed.

11. Sabon Sarkin ya fara soyayya da Camilla Parker Bowles tun 1986, a 2005 suka yi aure.

12. Camilla Bowles da Mai jiran gado suna zamansu ne a wajen fada kafin yanzu.

Kara karanta wannan

Alkali Ya Tura Dan Sufetan Yan Sanda Gidan Yari Kan Satar Motar N52m A Legas

13. A tarihin Wales, ba a taba yin Basaraken da ya dade a kan sarauta ba irinsa.

14. Sarki Charles III ya samu kyakkayawar alaka da shugabannin kasashen Duniya.

15. Tsohon Sarkin na Wales yana da jikoki biyar da ‘ya ‘yansa suka haifa.

Charles III ya zama Sarki

A baya kun ji labari bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth II, Yarima Charles, ya zama Sarkin Masarautar Ingila, ya gaji mulki yana 'dan shekara 73.

Fadar Buckingham ta sanar ranar da wannan a ranar Alhamis. Tun a jiya sabon Sarkin ya fitar da sanarwar farko a game da zaman makoki da aka fara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng