Sarauniyar Ingila, Elizabeth II Ta Kwanta Da, Ta Rasu Tana da Shekaru 96
- Allah yiwa sarauniyar Ingila Elizabeth II rasuwa bayan 'yar gajeriyar rashin lafiya da ta yi kwanan nan
- A yau ne aka kwantar da sarauniyar a asibiti, lamarin da ya jawo jimami da tashin hankali a kasar Ingila
- A shekarar da ta gabata ne mijin sarauniyar, Yarima Philips ya kwanta dama, kamar yadda rahotanni suka tabbatar
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Balmoral, Ingila - Yanzu muke samun labarin rasuwar sarauniyar Ingila Elizabeth II bayan 'yar gajiriyar rashin lafiya da aka sanar ta yi a yau Alhamis 8 ga watan Satumba.
Rahotanni daga majiyoyi sun shaida cewa, masarautar Ingila ta tashi bakin labarin jirkicewar lafiyar sarauniya, lamarin da yasa likitoci ke kai komo a kanta.
A wata sanarwar da masarautar ta Ingila ta fitar, an sanar da rasuwar sarauniyar da yammacin Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sarauniya ta kwanta dama cikin dadin rai a Balmoral da yammacin yau.
"Sarki da Sarauniya za su kasance a Balmoral a yammacin yau sannan su koma Landan a gobe."
A watan Afrilun shekarar da ta gabata ne mijinta Yarima Phillips ya rasu.
A 1952 ne Elizabeth II ta zama sarauniyar Ingila, a lokacin tana da shekaru 25 kacal.
A watan Yunin bana ne sarauniyar ta yi bikin cika shekaru 70 cif a kan karagar sarautar Ingila, kamar yadda kafar labarai ta CBC ta ruwaito.
Shekaru 70 kan karagar mulki: Sarauniyar Ingila ta kafa tarihin da aka jima ba’a gani ba
A ranar 6 ga watan Fabrairun bana ne Sarauniya Elizabeth II ta cika shekaru 70 a kan karagar mulkin Burtaniya.
Jaridar New York Times ta ba da rahoton cewa wannan ci gaba ya sanya sarauniyar cikin rukunin da ba a cika gani ba a tarihi, inda tarihi ya rubuta cewa, wasu sarakuna uku ne kawai aka san sun yi mulki sama da shekaru 70.
Kafar labarai ta CNN ta kara da cewa Elizabeth II, mai shekaru 95, ta zama sarauniyar Burtaniya ne bayan rasuwar mahaifinta King George VI a ranar 6 ga Fabrairu, 1952, yayin da take kasar Kenya a wani rangadi na kasa da kasa.
Yarima Philip, mijin Sarauniyar Ingila ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, Yarima Philip mijin Sarauniyar Ingila Elizabeth na II ya rasu yana da shekaru 99 a duniya kamar yadda fadar Buckingham Palace ta sanar a ranar Juma'a.
An wallafa sanarwar rasuwarsa ne a shafin Twitter na fadar sarautar Ingila @RoyalFamily.
"Cikin tsananin jimami Mai Martaba Sarauniyar Ingila ta sanar da rasuwar mijinta abin kaunarta, Mai girma Yarima Philip, Duke na Edinburg," a cewar sanarwar.
"Mai martaba ya rasu ne a safiyar yau Juma'a a Fadar Windsor.
Asali: Legit.ng