Daga Hawa Mulki, Firayim Ministar Ingila ta ba ‘Yar asalin Najeriya Kujerar Minista
- Kemi Badenoch ta zama sabuwar Ministar harkar kasuwanci bayan kafa sabuwar gwamnati a kasar Birtaniya
- Nasabar Badenoch tana dangantuwa da Najeriya, wannan mata mai shekara 42 babbar ‘yar siyasa ce a Ingila
- An haifi Badenoch a Kudancin Landan, kafin yanzu ta taba rike Ministar Baitul-mali da kananan hukumomi
United Kingdom - Liz Truss ta bada sanarwar nada Misis Kemi Badenoch a matsayin Ministar kasuwanci da kasashen ketare na kasar Birtaniya.
Sanarwar sabuwar Firayim Ministar Ingila watau Liz Truss ta fito ne a shafin ofishin shugaban Ingila a Twitter a ranar 6 ga watan Satumba 2022.
Baya ga kujerar Ministar kasuwanci, Kemi Badenoch mai shekara 42 za ta jagoranci majalisar kasuwanci ta Birtaniyar a matsayin shugabanta.
Rahoton Channels TV ya nuna an haifi Badenoch ne a matsayin Olukemi Olufunto a Wimbledon da ke Landan, asalin iyayenta mutanen Najeriya ne.
Kemi Badenoch ta kama aiki
Tuni Misis Badenoch ta shiga ofis kamar yadda ta shaida a dandalin Facebook, tace ta ji dadin ba ta wannan matsayi da Firayim Minista Truss tayi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sabuwar Ministar kasuwancin ta sha alwashin bada gudumuwarta wajen ganin dinbin mutane sun samu abin yi da sana’o’i a fadin kasar Birtaniya.
Tun a jiya ta halarci taron majalisar Ministoci, tace duk wata za ta rika wallafa bayanin cigaba da aka samu a mazabu da majalisa daga ma’aikatarta
Wacece Kemi Badenoch MP?
The Cable tace Badenoch ta karbi ma’aikatar kasuwancin ne daga hannun Anne-Marie Trevelyan wanda yanzu ta zama karamar Ministar harkar sufuri.
A watan Yulin 2022 Badenoch ta yi murabus daga kujerar Ministan daidaito da kananan hukumomi, kuma ta taba zama karamar Ministar Baitul-mali.
Kemi Badenoch MP ta shiga takarar zama Firayim Minista, amma ta zo ta hudu a zaben.
Atiku ya yi murna
Atiku Abubakar ya yi magana a shafin Facebook, yana taya ta murnar da wannan matsayi, yace wannan ya nuna inda gwamnatin Ingila ta sa gaba.
‘Dan takarar shugabancin na Najeriya yace nadin Kemi Badenoch MP ya kara tabbatar da matsayinsa na cewa Najeriya ta mori kwararru a Duniya.
Siyasar Najeriya
Dazu kun fahimci a tarihi, an yi lokacin da Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suka taimakawa Atiku Abubakar a zaben shugabancin kasa
A zaben 2023 da na 2015 ne kowa ya yi ta kan shi tsakaninsa da Atiku Abubakar, amma sai da kowanensu ya marawa Atiku baya a tafiyar siyasa.
Asali: Legit.ng