Kotun Saudi Ta Yankewa Tsohon Limamin Ka’aba Daurin Shekara 10 a gidan yari

Kotun Saudi Ta Yankewa Tsohon Limamin Ka’aba Daurin Shekara 10 a gidan yari

  • Saleh al Talib zai shafe shekaru 10 masu zuwa nan gaba a gidan kurkuku idan har an tabbatar da hukuncin da Alkali ya yi masa
  • Alkali ya samu shahararren malamin nan, Sheikh Saleh Al-Talib wanda ya yi limanci a ka’aba da laifi, ya yanke masa hukunci
  • Wata huduba da Al Talib ya yi a shekarun baya, ya soki bukukuwan da aka shigo da su, ya hada shi fada da gwamnatin Saudi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Saudi - A ranar Litinin, 23 ga watan Agusta 2022, wata kotu da aka kafa domin sauraron laifuffuka na musamman ta yanke hukunci ga Saleh al Talib.

Middle East Eye ta fitar da labari cewa an Sheikh Saleh al Talib da laifi, kuma an yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari a Saudi Arabiya.

Kotun daukaka karar ta yi fatali da hukuncin da aka yi a baya, inda aka wanke Sheikh Al Talib wanda tsohon limami ne a masallacin Harami a Makkah.

Kara karanta wannan

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

Hukumomin kasar Saudi Arabiya sun fara kama Saleh al Talib a 2018, a lokacin ba a bada wani dalili ba. Ana zargin wata hudubar da ya yi ta jawo kama shi.

A wancan lokaci, limamin ya yi Allah waidai da hukumar da gwamnati ta kafa domin kula da nishadi, ya kuma soki bukukuwan da aka shigo da su.

Kungiyar Dawn ta yi Allah-wadai

Kungiyar Dawn wanda Marigayi Jamal Khashoggi ya kafa, ta tabbatar da wannan hukunci da aka yankewa Saleh al Talib a shafin Twitter a makon nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limamin Ka’aba
Imam Saleh al Talib a Ka'aba Hoto: 21stcenturychronicle.com
Asali: UGC

Abdullah Alaoudh wanda shi ne Kakakin kungiyar ya yi tir da wannan hukunci, yake cewa Mohammed bin Salman ne ke neman rufe bakin malamai.

Gwamnati na kama Malaman Saudi

Rahoton yace Talib ya shahara a fadin Duniya, daga wajen Saudi Arabiya, dubban musulmai su na sauraron hudubobi da karatul Al-Kur’aninsa a Youtube.

Kara karanta wannan

Kisan Malami: Da Musulmai Suka Kashe Fasto, da Batun Ya Canza - Bala Lau Ya Dauki Zafi

Kima da martabar babban limamin bai hana a kama shi ba, yayin da Yarima Mohammed bin Salman yake kokarin kawo sauye-sauye a kasar Larabawan.

Ba wannan ne na farko ba, kafin yanzu, an ji labari gwamnatin Saudi ta cafke Salman al-Odah.

Jaridar Middle East Monitor tace kwanaki aka yanke hukuncin daurin shekaru 34 a gidan maza ga Salma al-Shehab saboda ya soki gwamnatin Saudi a Twitter.

Kisan malami a Najeriya

An ji rahoto ya zo cewa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tabbatar da cewa Musulmai ba za su yarda da kisan gillar da aka yi wa Sheikh Goni Aisami a jihar Yobe ba.

Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa Iqamatus Sunnah tana zargin ana yi wa Musulmai ta’addanci, tace dole ne a hukunta wadanda suka yi wannan aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel