Amurka Ta Kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden
- Shugaba Joe Biden, ya bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun kashe Ayman al-Zawahiri, Mutum na Biyu ga Osama Bin Laden a Afganistan
- Biden ya ce jami’an leken asirin Amurka sun gano inda al-Zawahiri yake a cikin farkon wannan shekara a lokacin da ya kai wa iyalin sa ziyara
- Al-Zawahiri wanda asali dan kasar Misira ne ya cigaba da jagorantar Al-Qaeda bayan mutuwar Osama bin Laden
Amurka - Shugaba Joe Biden, a jawabin da yayi wa manema labarai a yammacin jiya, ya ce umarnin kai hari da ya ba jiragen yakin Amurka a birnin Kabul na Kasar Afganistan yayi sanadiyar kashe al-Zawahiri.
Al-Zawahiri ya kasance jagora na farko ga tsohon shugaban Al-Qaeda, Osama bin Laden, wanda sojojin Amurka suka kashe a lokacin da yake buya a Pakistan a shekarar 2011.
Al-Zawahiri wanda asali dan kasar Misra ne ya cigaba da jagorantar Al-Qaeda bayan mutuwar Osama bin Laden.
A cikin jawabin nasa, Biden ya ce al-Zawahiri na da hannu dumu-dumu a harin ranar 11 ga watan Satumba, 2001, wanda ya kashe kusan Amurkawa 3,000, da kuma kitsa harin bam na USS Cole a shekara ta 2000, wanda ya kashe Amurkawa 17 na ruwa tare da jikkata wasu da dama.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Biden ya ce tun lokacin da al-Zawahiri ya karbi ragamar kungiyar Al-Qaeda daga hannun bin Laden, ya cigaba da juya lamuran kungiyar a fadin duniya inda yake fitar da bidiyoyin kira ga kai hari kan Amurka da kawayenta.
Ya ce jami’an leken asirin Amurka sun gano al-Zawahiri a cikin garin Kabul a farkon wannan shekarar a lokacin da ya je kai wa iyalansa ziyara.
Biden ya ce:
"A yanzu haka anyi adalci kuma mutanen duniya su daina jin tsoro saboda wannan shugaban na yan ta’adda baya nan domin an kashe shi.
Sokoto: Yadda Mutum 26 Suka Nutse A Ruwa Suka Mutu Sakamakon Gumurzu Da Yan Bindiga Da Jami'an Tsaro Suka Yi
A wan labari kuma, An gano gawarwaki a kalla guda 26 na mazauna kauyen Duma a karamar hukumar Tureta kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Rahotanni sun ce mutanen sun nutse ne a ruwa a yunkurin tserewa daga musayar wuta da ake yi tsakanin jami'an tsaro da yan bindiga a wani daji da ke kusa da su.
Asali: Legit.ng