Hotuna: Kakakin Majalisar Najeriya, Gbajabiamila Ya Koma Makaranta A Amurka

Hotuna: Kakakin Majalisar Najeriya, Gbajabiamila Ya Koma Makaranta A Amurka

  • Mr Femi Gbajabiamila, Kakakin Majalisar Wakilai Na Najeriya Ya Koma Makaranta a Jami'ar Jami'ar Harvard da ke Amurka
  • Gbajabiamila, a rubutun da ya wallafa tare da hotuna a shafinsa na Twitter ya ce furfura da yawan shekaru ba su hana neman ilimi
  • A yayin da ya ke Amurka yana kwas din a bangaren jagoranci/shugabanci, Mr Idris Wase, mataimakin kakakin majalisar ne zai rika jagorancin zaman majalisa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Femi Gbajabiamila, a halin yanzu yana karatun wani kwas a Makarantar Ilimin Koyon Aikin Gwamnati ta John F Kennedy da ke Jami'ar Kasuwanci ta Harvard.

Femi Gbajabiamila a aji.
Hotuna: Kakakin Majalisar Najeriya, Gbajabiamila Ya Koma Makaranta. Hoto: @femigbaja.
Asali: Twitter

Mr Gbajabiamila, wanda lauya ne, ya wallafa hotunansa a cikin aji tare da wasu daliban yan kasashen waje.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Dillalan jakuna: 'Yan Najeriya miliyan 3 za su rasa sana'a idan aka hana yanka jakuna

"Na koma aji. Yayin wani kwas na koyon dabarun jagoranci a @Harvard @Kennedy_School. Manta da yawan furfura da ke kai, yawan shekaru ba ya hanna neman ilimi, kaifafa basira ko fadada fahimta," ya rubuta a sahihin shafinsa na Twitter.

A lokacin da ya tafi karatun, mataimakin majalisar wakilai na tarayya, Idris Wase, shine ake sa ran zai cigaba da jagorancin zaman majalisar.

Ga hotunan Mr Gbajabiamila a makaranta a kasa:

Shugaban Majalisa ya roki Shugaba Buhari ya jarraba shawarwarin da Tinubu ya bada

A wani rahoton, shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya fito ya yi magana bayan Bola Tinubu ya bada shawarwarin magance matsalolin da ake fama da su.

Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya yi kira ga gwamnatin Muhammadu Buhari ta duba shawarwarin da Bola Ahmed Tinubu ya bada, sannan kuma ta yi aiki da su.

Jaridar Daily Trust ta ce Femi Gbajabiamila ya bayyana hakan ne ta bakin hadiminsa, Lanre Lasisi.

Kara karanta wannan

An samu hargitsi yayin da aka kama wasu 'yan sa kai na bogi a wurin zanga-zangar 'yan kwadago da ASUU

Mista Lanre Lasisi ya ce Femi Gbajabiamila ya na ganin akwai abubuwan da za a dauka a jawabin da Bola Tinubu ya yi a wajen bikin cikarsa shekara 69 da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164