Shin Shehu Shagari ya shugabanci Najeriya daga Lagas ne ko Abuja?
An zabi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari a matsayin Shugaban Kasan Najeriya daga 1979 zuwa 1983.
Shagari mai shekaru 92 ya fito daga kauyen Shagari dake jihar Sokoto.
A lokacin da yake mulki, kasar Najeriya ta soma shirin komar da babban birnin tarayya dake Lagas a waccan lokacin.
Shawarar ta bayyana ne yayinda jihar Legas ta soma samun cinkoson jama'a, wannan sanadiyan ne yasa aka nemi canjin wuri mafi girma domin kafa Babban birnin tarayya.
A wannan lokacin ne, al’umma da tattalin arzikin Lagas suka bunkasa sannan gwamnati ta dubi hanyoyin anfani da damar don bunkasa tattalin arzikin sauran sashin kasar.
Gwamnatin ta yi duba zuwa ga yankin dake nuni ga hadin kan kasa.
An zabi Abuja ta zama babban birnin tarayya saboda kasancewar birnin a tsakiyar yankunan kasa.
Ko da yake, mazaunan inda aka kafa babban birnin sun kasance yan kabilar Gbagi.
An samu rudani kan cewa ko Shagari ya mulki kasar daga Lagas ko Abuja.
Wannan rudanin bai kasance damuwa ba, ko da dai Janar Murtala Muhammed ne ya kawo shawarar dauke birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja (kafin zuwan mulkin Shagari) amman an cin ma burin ne 1991 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Asali: Legit.ng