Sunaye, hotuna da bidiyoyin kira'ar limamai 6 na Masallacin Annabi da ke Madina

Sunaye, hotuna da bidiyoyin kira'ar limamai 6 na Masallacin Annabi da ke Madina

Ba tare da tantama ba, zama limamin masallacin Annabi shi ne abu mafi girma, karramawa da alfahari a duniyar Musulunci baki daya. Ba kowa Allah madaukakin Sarki ke bai wa irin wannan damar da karamar ba.

Jerin sunaye da hotunan limami 6 na Masallacin Annabi da ke Madina
Jerin sunaye da hotunan limami 6 na Masallacin Annabi da ke Madina. Hoto daga lifeinsaudiarabia.net
Asali: UGC

Sharuddan zama limamin masallacin Annabi

Duk da gwamnatin Saudi Arabiya ce ke nada limamai, dole ne a cike wadannan ka'idojin hudu kafin zama limamin masallacin Annabi, kamar yadda Argaam suka ruwaito.

  1. Kasancewar mutum mazaunin kasar Saudi na dindindin.
  2. Kaiwa shekaru 30 ko sama da haka.
  3. Mallakar digiri a fannin shari'a daga wata jami'ar Saudi.
  4. Haddace Qur'ani da kira'a mai dadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sheikh Abdul Mohsen Al Qasim

An haifi Sheikh Abdul Mohsen bin Muhammad bin Abdul Rahman bin Muhammad bin Abdullah bin Qasim a 1968 sannan ya haddace kur'ani da karancin shekaru.

Kara karanta wannan

Tsohon zakaran kwallon Afrika, Patrick Mboma, ya musulunta kuma kai tsaye aka aura masa amarya

Ya mallaki kwalin digiri a fannin shari'ar musulunci, sannan an nada shi a matsayin limamin masallacin Annabi a shekarar 1997.

2. Sheikh Saleh Al Badir

An haifi Sheikh Saleh Al Badir a shekarar 1970 a Hofuf. Ya yi digirinsa na farko a fannin shari'a daga jami'ar musulunci ta Muhammad Bin Saud.

An nada shi a matsayin limamin, kuma mai wa'azi a masallacin Annabi a shekarar 1998. Ya dauki tsawon lokaci yana jagorantar sallolin Tarawihi a masallacin Annabi tun shekarar 2005.

3. Sheikh Ahmed Bin Humaid

An haifi Sheikh Ahmed Bin Talib bin Abdul Hamid bin Al Muzaffar Khan a shekarar 1980 a Riyadh. Ya yi digirin digirgirgir a fannin da ya shafi shari'a daga babbar cibiyar shari'a.

An nada shi a cikin watan Ramadanan shekarar 1434 don ya jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Annabi, daga bisani aka nada shi limami a ranar 9 ga watan Oktoba, 2013.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban ƙasa Buhari ya naɗa sabon shugaban masu yi wa kasa hidima NYSC

4. Sheikh Abdullah bin Abdul Rahman

A halin yanzu, Abdullah bin Abdul Rahman bin Suleiman Al-Baijan na limancin masallacin Annabi, sannan yana daya daga cikin mambobin reshen jami'ar musulunci ta Madina.

An nada shi a matsayin limamin masallacin Annabi a shekarar 2013, sannan ya yi digirin digirgirgir a sashin shari'ar siyasa daga jami'ar musulunci ta Imam Muhammad bin Saud a shekarar 2015.

5. Sheikh Khaled Al Muhanna

An haifi Khalid bin Suleiman bin Abdullah bin Suleiman bin Muhanna Al-Shamkari a Al Ahsa a shekarar 1976. Ya yi digirin digirgirgir daga jami'ar musulunci ta Imam Muhammad bin Saud a shekarar 2010.

An nada Sheikh Khalid Al Muhanna a matsayin limamin masallacin Annabi a ranar 13 ga watan Oktoba 2019.

6. Sheikh Ahmed bin Ali Al-Hudhaifi

Sheikh Dr. Ahmed bin Ali Al-Hudhaifi limami ne, kuma mai bada shawara, sannan wakilin dake kula da jagoranci da al'amuran babban masallacin Annabi.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram

A wani labari na daban, hukumomin kasar Saudiyya sun saki sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami dake Makkah na watan Ramadanan wannan shekarar. Sakin jerin sunayen limaman yazo ne ta shafin a ranar 23 ga watan Maris.

Jerin sunayen limaman da zasu jagoranci sallar Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami sun hada da.

Asali: Legit.ng

Online view pixel