Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban NYSC na ƙasa

Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban NYSC na ƙasa

  • Shugaban ƙasa Buhari ya naɗa Birgediya Janar Mohammed Fada, daga jihar Yobe a matsayin sabon shugaban NYSC ta ƙasa
  • Sabon shugaban zai karɓa ne daga hannun DG mai barin gado, Manjo Janar Shu'aibu Ibrahim, wanda wa'adinsa ya ƙare
  • Bayanai sun nuna cewa sabon DG ɗin ya ziyarci hedkwatar NYSC don samun bayani kan yadda abubuwa ke tafiya yau Talata

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya amince da naɗin Birgediya Janar, Mohammed Fada, a matsayin sabon Darakta Janar na yan yi wa ƙasa hidima NYSC.

Janar Fada wanda ya fito daga jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya zai karɓi ragama ne daga hannun Manjo Janar Shuaibu Ibrahim, wanda ya kammala wa'adi biyu.

Shugaba Buhari ya naɗa sabon DG NYSC.
Da Dumi-Dumi: Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban NYSC na ƙasa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Wata majiya mai ƙarfi ce ta shaida wa wakilin jaridar Punch wannan cigaban ranar Talata 17 ga watan Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Fashewar tulun iskar gas: Hukuma ta bayyana adadin mutanen da suka mutu a iftila'in Kano

Majiyar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Gwamnatin Buhari ta amince da naɗa sabon Darakta Janar na NYSC, kuma wanda Allah ya ba shi ne Birgediya Janar Mohammed Fada daga jihar Yobe."
"Sabon DG ɗin ya ziyarci hedkwatar NYSC ranar Talata kuma DG mai barin gado, Manjo Janar Shu'aibu Ibrahim, ya masa bayani."
"Bayan Faretin bankwana Ibrahim zai miƙa ragama ya tafi, yana da kyau lokacin da zaka bar wuri, kamata ya yi aga hawayen farin ciki na kwaranya maimakon a ga mutane na Alla-Alla ka tafi, wa'adin shekara uku kamar shekara 20."

Waye DG mai barin gado?

DG mai barin gado, Manjo Janar Ibrahim, haifaffen ƙaramar hukumar Nasarawa ne a jihar Nasarawa, yana matsayin kusa da zama Farfesa a fannin Tarihi da ilimin yaƙi a makarantar horon Sojoji ta Najeriya.

Ya fara aiki a matsayin DG na NYSC a watan Mayu, 2019 kuma kafin zuwa wannan muƙamin shi ne Rijistara na jami'ar sojojin ƙasa da ke Biu, jihar Borno.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun aike da sakon sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

Ya gama digirinsa na farko a fannin Tarihi a 1989, digiri na biyu a Tarhihi a 1992 duk a jami'an UNIJOS kuma ya gama digiri na uku a Fannin dai na Tarihi a Jami'ar Abuja a shekarar 2007.

A wani labarin kuma An fara harbe-harben bindiga a wurin da 'Tukunyar Gas' ta fashe a Kano

Ƙarar harbe-harben bindiga ya tashi sosai a a wurin da tukunyar Gas ta fashe a yankin Sabon Gari, jihar Kano ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro ne suka saki harbin domin tarwatsa dandazom mutanen da suka mamaye wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel