Wata sabuwa: Saudiyya ta haramta daukar ruwan Zam-Zam zuwa wasu kasashe
- Kasar Saudiyya ta haramtawa jiragen sama daukar ruwan zam-zam a jakukkunan fasinjoji zuwa wasu kasashe
- Wannan na zuwa ne daidai lokacin da ake jiran shigowar watan Zul-Hajj da musulmi ke taruwa a kasar ta Saudiyya
- Hukumar ya fitar da sanarwa mai dauke da ka'idojin da gwamnati za ta dauka kan masu saba sabuwar dokar
Kasar Saudiyya - Rahoton BBC ya ce, jukumomin sufurin jiragen sama na Saudiyya sun hana daukar ruwan Zamzam a cikin jakar daukar kaya yayin da ake tunkarar watan Zul Hajj, wata mai alfarma na aikin Hajjin Musulunci.
Hukumar ta fitar da sanarwar a hukumance game da sabon tsarin, wanda ke hana mahajjata daukar Zamzam - ruwan rijiyar Zamzam zuwa kasashensu.
An nemi dukkan kamfanonin jiragen sama da su ke tabbatar da cewa babu wani daga cikin fasinjojinsu da ke tafiya ta Jeddah ko wani filin jirgin sama na kasar Saudiyya da ke da robobin ruwan na Zamzam.
Ba Zan Bari Maƙiyan El-Rufai Su Kawo Mana Cikas a Hajjin 2022 Ba, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai
Za a dau mataki kan kamfanonin jiragen sama idan suka saba wa sabbin umarni, kamar yadda rahoton Geo.tv ya bayyana.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ruwan Zamzam dai shi ne ruwan rijiyar da ke cikin Masallacin Harami na Makkah, wanda ya kasance tushen ruwa mai cike da mu'ujiza kamar yadda tarihin Musulunci ya nuna.
Ruwan yana da matukar daraja a addini kuma mutane suna daukarsa zuwa kasashensu da yawa bayan sun kammala aikin Hajji ko Umra.
Kalli sanarwar:
Hukumomin Saudiyya sun haramta wa mazan kasar auren matan Pakistan
A wani labarin makamancin wannan, an haramta wa mazan Saudi auren daga auren matan Pakistan, Bangladesh, Chadi da Burma.
Life in Saudi ta ruwaito cewa, an sanar da hakan ne don hana mazan Saudi karfin guiwar auren mata daga kasashen ketare.
'Yan kasar Saudi dake son auren matan kasashen ketare, da farko dai za su nemi takardar shaidar amincewa daga sananniyar hukumomin gwamna, tare da shigar da bukatar auren a inda ya dace.
Manjo janar Assaf Qureshi, wanda shi ne daraktan 'yan sandan Makkah ya ce, duk wani shigar da bukatar aure daga wajen masarautar zai bi ta hanyoyin lura da tsanani kafin a amince ko a ki amincewa da shi.
Daga nan ne kwamitin za ta yanke shawarar amincewa ko rashin amincewa da hakan.
A wani labarin kuma, wani mutumi 'dan nahiyar Afirka ya siyar da gidan da shi kadai ya mallaka don yayi Umara. Kai ziyara kasa mai tsarki ta Makkah don yin aikin Hajji da Umara shine burin dukkan musulman fadin duniya.
Sai dai, zuwa kasa mai tsarkin na bukatar tanadi da dama. Ba niyya mai karfi kadai ba, bauta a birnin mai tsarki na bukatar isashiyar lafiya, hankali, lokaci da kuma dukiya.
Kudin da ake bukata don gudanar da wannan bautar babu shakka ba kudi bane kalilan.
Asali: Legit.ng