Yadda tsoho dan Afrika ya siyar da gidansa tilo, ya tattara ya tafi Umra da Hajji

Yadda tsoho dan Afrika ya siyar da gidansa tilo, ya tattara ya tafi Umra da Hajji

  • Wani mutumi 'dan Afirka ya saida gida daya tilo daya mallaka don samun damar zuwa kasa mai tsarki yayi Umara a watan Ramadanan wannan shekarar
  • A bidiyon da yayi yawo a shafukan sada zumuntar zamani na Twitter, wani 'dan jaridar kasar Kuwait mai suna Nayef Al Rashidi ya wallafa, na bayyana zantawarsa da tsohon a babban masallacin Annabi
  • Al Rashidi ya bukaci jama'an Annabi da su nunawa tsohon halin karamci ta hanyar tallafa masa da abunda Ubangiji ya ba su, duba da irin babbar sadaukarwa da yayi

Wani mutumi 'dan nahiyar Afirka ya siyar da gidan da shi kadai ya mallaka don yayi Umara.

Kai ziyara kasa mai tsarki ta Makkah don yin aikin Hajji da Umara shine burin dukkan musulman fadin duniya. Sai dai, zuwa kasa mai tsarkin na bukatar tanadi da dama. Ba niyya mai karfi kadai ba, bauta a birnin mai tsarki na bukatar isashiyar lafiya, hankali, lokaci da kuma dukiya.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah tayi Allah wadai da zagin Annabi (SAW) da wata yarinya tayi a jihar Sokoto

Yadda tsoho dan Afrika ya siyar da gidansa tilo, ya tattara ya tafi Umra da Hajji
Yadda tsoho dan Afrika ya siyar da gidansa tilo, ya tattara ya tafi Umra da Hajji. Hoto daga theislamiceinformation.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kudin da ake bukata don gudanar da wannan bautar babu shakka ba kudi bane kalilan.

Saboda haka, musulmai da dama basa samun damar yin aikin Hajji ko mahimmiyar tafiya zuwa Makkah saboda matsalar rashin kudi. Mutane da dama suna fafutuka, gami da tara kudi tsawon shekaru don tara kudin tafiyar mai albarka.

Sai dai ba tare da zato ko tsammani ba, an samu labarin wani musulmi 'dan Afirka da yayi fafutukar ganin ya je kasa mai tsarkin. Duk da kasancewarsa ba mai hannu da shuni ba, daga karshe dai tsohon ya samu damar zuwa birni mai tsarki na Makkah don yin Umara a wannan watan Ramadanan bayan yayi babbar sadaukarwa.

Wani 'dan jaridar kasar Kuwait, Nayef Al Rashidi ne ya fara wallafa labarin mai kara kwarin guiwan ta hanyar amfani da wani bidiyon, wanda daga bisani ya yadu a kafafan sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

A bidiyon da ya wallafa, an ga Rashidi yana tattaunawa da wani tsoho dake zaune kusa da shi yayin da suke cikin babban masallacin.

Mutumin shi ne tsohon da ya siyar da gida da shi kadai ya mallaka don ya samu damar zuwa Umara a watan Ramadanan wannan shekarar.

A wallafarsa ta Twitter, Al Rashidi ya kammala bidiyon da tsokaci a harshen larabci wanda ke nufin: "Ya siyar da gidansa don zuwa Makkah yayi Umara. Ubangiji ya sa masa albarka, gami da maye masa da gida a aljanna."

Mutane da dama a shafukan sada zumuntar sun amince a tsokacin da Al Rashidi yayi. Halayyarsa ta girgiza su, sannan sun sanya wa tsohon albarka da irin babbar sadaukarwar da yayi. Babu shakka ya kafa misalin fifita lahira a kan duniya.

Ba dole ya mallaki gidan kansa idan ya dawo daga kasar ba, amma tabbas yayi wa kansa babban tanadi a lahira. Al Rashidi ya bukaci mutane da su nuna wa mutumin halin karamci ta hanyar tallafa masa gwargwadon hali.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Ana dab da Iftar, magidanci a Saudiyya ya kone iyayensa, iyalinsa da gidansa kurmus

A wani labari na daban, Ana dab da buda baki, wani mutumi ya garkame mahaifinsa, mahaifiyarsa, 'dansa da 'diyarsa, wadanda ke azumi a gidan a Saudiyya gami da banka wa gidan wuta.

Wutar ta fara ci ne sanadiyyar man fetur da aka antaya wa gidan, gami da banka wa gidan wuta, wanda ya lashe rayukan mutane hudu: mahaifinsa, mahaifiyarsa, karamin yaronsa da 'diyarsa.

Mummunan lamarin ya auku ne a Safwa, kusa da Qatif, inda gobarar ta balle ana dab da buda baki. Iyalin basu tsira daga kunar wutar ba, inda ya rufesu da gan-gan a wani daki don hana su guduwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel