Bai Kamata Ku Yi Ramadan Ku Kaɗai Ba: Waɗanda Ba Musulmi Ba Sun Taya Musulmin Saudiyya Azumi

Bai Kamata Ku Yi Ramadan Ku Kaɗai Ba: Waɗanda Ba Musulmi Ba Sun Taya Musulmin Saudiyya Azumi

  • Wadanda ba musulmi ba a kasar Saudiyya sun yi azumin watan Ramadan tare da abokan zamansu a kasa mai tsarki
  • Wasu daga cikin mutanen da ba musulmi ba sun ce azumin na Ramadan wata dama ce ta karfafa abokantaka da karamci tsakaninsu da musulmi
  • Rahotanni sun nuna cewa mutanen da ba musulmi ba a kasar ta Saudiyya suna cigaba da kara rungumar al'adun mutanen na Saudiyya

Saudiyya - Al'ummar da ba musulmi ba mazauna kasar Saudiyya sun yi azumin watan Ramadan tare da musulmi da nufin kara dankon zumunci da abota tsakaninsu da musulmi, rahoton BBC Hausa.

Arab News ta wallafa a shafinta cewa sun dauki azumi, sun kuma kiyayye dokokinsa sannan sun sha ruwa tare da abokansu musulmi a kasar mai tsarki.

Bai Kamata Ku Yi Ramadan Ku Kaɗai Ba: Waɗanda Ba Musulmi Ba Sun Taya Musulmin Saudiyya Azumi
Bai Kamata Ku Yi Ku Kaɗai Ba: Waɗanda Ba Musulmi Ba Sun Taya Musulmin Saudiyya Azumi. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Azumi na kara mana kusanci da abokan zaman mu musulmi, Wadanda ba musulmi ba

Kara karanta wannan

Jami'an tsaron Saudiyya sun cafke 'yan Pakistan 150 da suka yi ihun take siyasa a Masjid Annabawi

Jaridar ta rahoto daya daga cikinsu yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bai kamata ku yi Ramadan ku kadai ba - wannan lokaci ne na karfafa abota da karamci a tsakaninmu."

Daga cikin wadanda suka yi azumin tare da musulmi sun furta cewa azumin ya kara musu kusanci tare da abokan zamansu musulmi.

Rahoton da jaridar ta wallafa ya ce duk da banbancin addini, wasu yan kasashen waje wadanda ba musulmi ba suna kara rungumar al'adun mutanen Saudiyya.

Baya ga zamansa ibada ga al'ummar musulmi, wasu binciken masana kimiyya sun nuna cewa yin azumi na kauracewa ci da sha daga fitowar al fijrzuwa faduwar rana yana taimakawa wurin inganta lafiyan jikin bil'adama.

Sallah: Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Duba Jinjirin Wata

A wani labarin, Kwamitin Kolin Harkokin Addinin Musulunci, NSCIA, karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ta taya musulmi murnar Sallah Karama da kammala azumin watan Ramadan, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Kalaman Sarkin Waka: Mun yi dawafi a kanka, mun hada ka da Allah, Jarumai maza a Saudiyya

A cikin sanarwar da Direktan Gudanar Da Ayyuka, Zubairu Usman-Ugwu ya fitar a ranar Juma'a, NSCIA ta umurci musulmi su aiwatar da darrusan da suka koya a ramadan, wanda shine tallafawa marasa karfi.

Ana bikin sallah karama ne a kowanne shekara bayan kammala azumin watan Ramadan a duk fadin duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel