Ango ya sha da kyar bayan Amaryar sa ta kusa kashe sa da makami

Ango ya sha da kyar bayan Amaryar sa ta kusa kashe sa da makami

- Wata Mata ta kusa aika Mijin ta a Garin Sokoto

- An dai yi wa wannan Baiwar Allah auren dole ne

- Ya kamata a rika aurawa Jama’a masu kaunar su

Labari ya kai gare mu daga Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN cewa an dai kuma samun wata Amarya da ta kai wa Mijin ta hari kwanan nan inda ta kusa hallaka sa a cikin Garin Sokoto.

Angon mai suna Umar Shehu ya sha da kyar ne bayan da Amaryar sa ta kusa kashe sa inda ta nemi ta dadara masa reza tsirara a kan sa. Wannan abu dai ya faru a Unguwar Arkillar Liman a Karamar Hukumar Wammako a Garin Sokoto Sokoto.

KU KARANTA: Wasu yara sun kashe sa'an su a Garin Bauchi

Wannan abin takaici ya faru ne a karshen makon nan inda Shafa Muhammadu mai shekaru 28 ta yanke hukuncin ganin karshen mijin ta na aure. Labari ya zo mana cewa auren dole aka yi wa wannan Baiwar Allah da Malam Umar Shehu.

Yanzu haka dai har an sallame sa daga asibiti don kuwa raunin da ya samu bai kai ya kawo ba. Jami’an ‘Yan Sandan Jihar da kuma dangin ma’auratan su ka tabbatar da wannan. Angon dai ya ga ta kan sa ne lokacin da ya leka dakin sahibar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: