Fitaccen Malami a Saudiyya ya ce babu laifi yin bikin ranar zagayowar haihuwa a Musulunci

Fitaccen Malami a Saudiyya ya ce babu laifi yin bikin ranar zagayowar haihuwa a Musulunci

  • Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, ya ce a musulunce babu laifi idan musulmi ya yi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ko na masoyansa
  • Kamar yadda malamin, wanda tsohon mamba ne a kungiyar manyan malaman Saudi Arabiya ya ce, hakan bai da wani laifi a musulunci
  • Haka zalika ya kara da cewa, abunda musulunci bai amince dashi ba shine kirkirar abu wanda baya daga cikin al'amarin addini

Riyadh - Dr. Qais Bin Muhammad Al-Sheikh Mubarak, tsohon mamban kungiyar manyan malaman Saudi Arabiya, ya ce babu laifi idan musulmi ya yi murnar shagalin bikin al'ada irin su, murnar zagayowar haihuwarsa ko na masoyansa.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa, hakan bai da bambamci da murnar zagayowar ranar aure, samun karin girma ko matsayin mutum ko na 'ya'ya, samun damar kammala digiri ko kammala karatu daga jami'a, ko sauran bukukuwa, a cewarsa.

Kara karanta wannan

Matsaloli ta ko ina: Najeriya na bukatar shugabanni masu tsoron Allah, inji malamin addini

Fitaccen Malami a Saudiyya ya ce babu laifi yin bikin ranar zagayowar haihuwa a Musulunci
Fitaccen Malami a Saudiyya ya ce babu laifi yin bikin ranar zagayowar haihuwa a Musulunci. Hoto daga saudigazette.com.sa
Asali: UGC

Kamar yadda Al-Mubarak ya bayyana, babban abu game da bukukuwan nan shine, abubu aya ko hadisi da ya halasta ko ya haramta hakan. Ya dauki wadannan tarukan a matsayin wani bangare na al'ada, wadanda basu da wani aibu a addinance. Basa cikin abubuwan da aka haramta a Qur'ani ko hadisin Annabi (Tsira da aminci su tabbata a gareshi).

Al-Mubarak ya yi nuni da cewa wadannan abubuwan basu shafi wani bangare na addini ba, inda ba'a amince da karawa ko rage wani abu ba. Duba da maganar Annabi na cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Duk wanda ya kirkiri wani abu a lamarin nan namu (Musulunci) wanda baya ciki, ba za'a amince dashi ba."

Saboda haka, Malamai sun amince ba tare da sabani ba da haramta sabon salon bauta da ya zarce bautar da aka wajabta a Qur'ani mai Girma ko Sunnar Annabi, irinsu kara wata sallah ta shida a kan salloli biyar na rana, a cewar Al-Mubarak.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game shugaban cibiyar Kididdigan Najeriya da ya mutu yau

Ya tunatar da cewa, babu laifi idan an yi amfani da damar yin kowanne abu kamar Hijirar da Annabi ya yi ko wasu abubuwa don tunatarwa, shiryatarwa da jagorantar da Musulmai a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram

A wani labari na daban, hukumomin kasar Saudiyya sun saki sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami dake Makkah na watan Ramadanan wannan shekarar. Sakin jerin sunayen limaman yazo ne ta shafin a ranar 23 ga watan Maris.

Jerin sunayen limaman da zasu jagoranci sallar Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami sun hada da:

Sheikh Abdullah Awad Al Juhany

Sheikh Abdur Rahman Al Sudais

Sheikh Saud Al Shuraim

Sheikh Maher Al Muaiqly

Sheikh Yasir Al Dawsary

Sheikh Bandar Baleelah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel