Ku shafawa kanku ruwa: Meta ya gargadi masu barazanar kashe shugaban Rasha Vladimir Putin a Facebook

Ku shafawa kanku ruwa: Meta ya gargadi masu barazanar kashe shugaban Rasha Vladimir Putin a Facebook

  • Facebook ya gargadi masu amfani da shafukansa a Rasha game da barazanar tada hankali ko yunkurin kashe shugaba Vladimir Putin na Rasha
  • Kamfanin ya ce sassauta ka'idojin kalaman nuna kyama a kasashe uku na Gabashin Turai an yi shi da nufin ba 'yan Ukraine damar bayyana fushinsu game da mamayar Rasha
  • Facebook ya fada a cikin wata sanarwa cewa kamfanin ba zai lamunci ganin barazana ko wata magana da bata dace ba

Tushen Facebook da Instagram, wato Meta ya ce mutane bai kamata su ke rubutu ko jawabai masu kira ga mutuwar shugaban Rasha, Vladimir Putin ko kowane shugaban kasa ba, kamar yadda CNBC ta ruwaito.

Kamfanin ya ce rahoton ya sassauta ka'idojinsa na nuna kyama ya shafi rubuce-rubuce ne daga 'yan Ukraine da barazanar kai hari ga sojojin Rasha da kuma yin jawabi bisa mamayar Rasha a Ukraine.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha Da Ukraine Na Iya Tsananta Talauci a Najeriya, Oxfam Ta Yi Gargadi

Shugaban Rasha, Putin na shan barazanar kisa a Facebook
Ku shafawa kanku ruwa: Meta ya gargadi masu barazanar kashe shugaban Rasha Vladimir Putin a Facebook | Hoto: Mikhail Klimentyev/AP

Meta ya yi karin bayani game da sauya ka'idojinsa

Batun inji Meta ya zama dole bayan da Reuters ya ba da rahoton cewa Meta ya sauya ka'idojinsa a Rasha, Ukraine da Poland domin ba da damar fadin barazana ga shugaban Belarus, Alexander Lukashenko saboda mamayar sojojin Rasha a Ukraine.

A cewar rahotannin kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Alhamis, 17 ga Maris, 2022, Facebook ya amince da yin bore ga sojojin Rasha a wadannan kasashe uku da wasu kasashen Gabashin Turai da dama da Yammacin Asiya.

Rasha ta mayarwa da Facebook martani

Kasar Rasha ta bude wani shafin kai karar laifuka kan Meta a ranar Juma'a, 18 ga Maris, 2022, saboda sauyin ka'idojinsa na kalaman kyama.

Rasha ta hana jama'arta damar shiga Instagram tare da toshe Facebook bayan mamayarta a Ukraine yayin da Facebook ya hana wasu manyan kafofin watsa labaru masu alaka da gwamnati aiki.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An rasa rai 1 yayin da tankar mai ta yi arangama da tirela a Kano

A cewar wani sako a ranar Lahadi, jigo a kamfanin Meta, Nick Clegg ya bayyana cewa, yana mai jawo hankalin jama'a cewa, Meta bai sauya ka'idoji a yankunan don ba da damar tada zaune tsaye ba.

Rasha ta aika muhimmin sako ga daliban Najeriya, ta basu guraben karatu

A wani labarin, ma'aikatar Ilimi ta kasar Rasha ta shaida wa yan Najeriya cewa a shirye ta ke ta basu guraben karatu idan suna sha'awar cigaba da karatunsu a kasar.

Mikhail L. Bogdanov, Shugaban Rasha na Kasashen Tsakiya da Afirka kuma mataimakin Ministan Harkokin Kasashen Waje na Rasha ne ya sanar da hakan.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da jakadan Najeriya a Rasha, Abdullahi Shehu, kamar yadda Channels TV ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.