Rasha Ta Aika Muhimmin Saƙo Ga Ɗaliban Najeriya, Ta Basu Guraben Karatu

Rasha Ta Aika Muhimmin Saƙo Ga Ɗaliban Najeriya, Ta Basu Guraben Karatu

  • Rasha ta ce a shirye ta ke ta bawa yan Najeriya guraben karatu idan suna sha'awar cigaba da karatunsu a can kasar
  • Kasar ta kuma ce za ta cigaba da bada taimakon da ya dace domin tabbatar da tsaro da walwalar yan Najeriya da ke Rasha
  • Mikhail Bogdanov, mataimakin ministan harkokin kasashen waje na Rasha, ne ya bada tabbacin yayin wani taro da Abdullahi Shehu, jakadar Najeriya a kasar

Ma'aikatar Ilimi ta kasar Rasha ta shaida wa yan Najeriya cewa a shirye ta ke ta basu guraben karatu idan suna sha'awar cigaba da karatunsu a kasar.

Mikhail L. Bogdanov, Shugaban Rasha na Kasashen Tsakiya da Afirka kuma mataimakin Ministan Harkokin Kasashen Waje na Rasha ne ya sanar da hakan.

Kara karanta wannan

Yakin Rasha da Ukraniya: An kashe yan jaridan Fox News biyu, an cirewa daya kafa

Rasha Ta Aika Muhimmin Saƙo Ga Ɗaliban Najeriya, Ta Basu Guraben Karatu
Rasha Ta Aike Da Muhimmin Saƙo Ga Ɗaliban Najeriya, Ta Basu Guraben Karatu. Hoto: Femi Adesina
Asali: UGC

Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da jakadan Najeriya a Rasha, Abdullahi Shehu, kamar yadda Channels TV ta rahoto.

Bogdanov, wanda ya tarbi jakadan na Najeriya a ofishinsa, ya tabbatarwa Shehu cewa Rasha za ta bada taimakon da ya dace don tabbatar da tsaro da walwalar daliban Najeriya mazauna Rasha.

Hakan na zuwa ne yayin da rikici ya barke tsakanin Rasha da Ukraine da ya yi sanadin mutane da dama suna tserewa daga Ukraine.

Ya kara da bawa jakadan Najeriyan tabbacin cewa Rasha ta dauki Najeriya a matsayin kasa mai muhimmanci a Africa kuma za ta cigaba da karfafa dankon zumunci da ita.

Martanin Jakadan Najeriya, Abdullahi Shehu

A martaninsa, Farfesa Abdullahi Shehu ya mika godiyarsa ga Gwamnatin kasar Rasha kan damuwar da ta nuna ga halin da yan Najeriya ke ciki.

Kara karanta wannan

Tattalin arziki: Najeriya na fuskantar barazanar asarar sama da Naira Biliyan 1 a kullum

Jakadan ya kuma kara da mika bukatarsa ga Rasha na cewa ta bada taimako da kulawa da yan Najeriya da ke Rasha tare da karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG

A bangare guda, Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa ‘yan Najeriya baza su cutu ba a rikicin da ke ta ballewa tsakanin kasar Rasha da Ukraine, The Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya samu damar ganawar sirri da jakadan ya shaida wa Shebarshin cewa Najeriya kawar Rasha ce.

A cewar Onyeama, yayin tattaunawa da Shebarshin ya sanar da shi cewa Najeriya baza ta lamunci cin zarafin kasa da kasa ba daga wata kasar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, kasar da ke da jakada a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsadar man fetur: Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel