Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

  • Wani jami'in Amurka ya bayyana cewa, kasar Belarus na shirin tura dakaru domin taimakawa kasar Rasha a yunkurinta na mamaye kasar Ukraine
  • Wannan dai na zuwa ne jim kadan bayan wani zaben raba gardama a kasar Belarus ya amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar kan batun nukiliya
  • A halin da ake ciki kuma, an ce an ga dakarun na musamman na Belarus suna cike jiragen sama a shirinsu na kai hari ta sama kan birnin Kyiv na Ukraine

Ukraine - A yayin da ake ci gaba da yin Allah wadai da mamayar da kasar Rasha ta yi wa kasar Ukraine, Belarus na shirin tura dakaru domin taimakawa shugaba Vladimir Putin domin yakar Ukraine, in ji rahoton Washington Post.

Kara karanta wannan

Babu shugaba da mataimaki a kasa: Osinbajo ya keta hazo bayan shillawar Buhari Faris

Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Belarus Alexander Lukashenko abokan kawance ne na kud-kud. Rahotanni sun kuma nuna cewa, ana kyautata zaton barin sojojin Belarus zuwa Ukraine a yau Litinin 28 ga watan Fabrairu.

Kasar Belarus ta shiga yakin Ukraine da Rasha
Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin mamaye Ukraine | Hoto: Reuters
Asali: UGC

An bayyana hakan ne jim kadan bayan da wata kuri'ar raba gardama a Belarus ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya rushe matsayin kasar na kasancewa mara hulda da nukiliya - hakan na nufin kasar za ta iya daukar nauyin makaman Rasha.

An san Lukashenko a matsayin dan kama-karya na karshe a nahiyar Turai, kuma yana kan karagar mulki tun 1994.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Galibin kasashen duniya sun yi imanin cewa ya kan murde zabe domin tabbatar da cewa ya yi nasara, kuma a 2020, masu zanga-zangar sun fito kan tituna suna zargin Lukashenko da murde zaben shugaban kasa; an kama dubban mutane aka yi musu dukan kawo wuka.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Ukraine da Rasha za su yi zaman tattaunawar sulhu, an fadi inda za a gana

Daily Mail ta kara da cewa an ga dakaru na musamman na Belarus suna shiga jiragen sama a shirye-shiryen kai hari ta sama kan birnin Kyiv a wani lamari da ke nuna fadada yakin, in ji majiyoyin soja.

Ba a bayar da bayanin adadin sojojin da kuma inda za a tura su ba. Duniya dai na ci gaba da daurawa Rasha laifin tada yakin, kuma kasashe da dama sun kakabawa gwamnatin Rasha takunkumi.

'Yan Najeriya a Ukraine: Aisha Buhari ta mika kokon bara ga Buhari a madadin 'yan Najeriya

A wani labarin, kokarin da jami’an diflomasiyyar Najeriya ke yi na ganin an kwashe ‘yan Najeriya da suka makale a kasar Ukraine da yaki ya dumfara ya sha yabo daga Aisha Buhari.

Sai dai, a cikin wani sakon da ta wallafa a Facebook a ranar Lahadi, 27 ga watan Fabrairu, uwargidan ta shugaban Najeriya ta yi kira ga kwamitin shugaban kasa kan yaki da Korona da ta yafe kudin gwajin Korona ga 'yan Najeriyan da suke dawowa daga kasashen Turai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Ta kuma roki a soke karbar irin wadannan kudade ga duk yaran Najeriya da ke dawowa gida nan ba da dadewa ba, tare da rage kudin gwajin ga dukkan ‘yan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.