'Yan fashi sun kacame da rikici suna tsaka da fashi, sun halaka junansu da makamansu

'Yan fashi sun kacame da rikici suna tsaka da fashi, sun halaka junansu da makamansu

  • Wasu gungun 'yan fashi da makami sun haura wata mashaya a ranar Asabar da ta gabata wurin karfe 3 na dare inda suka yi wa maigadi duka tare da daure shi
  • Sai dai bayan sun sha giya sun yi tatul tare da debo wasu da za su tafi da su, rikici ya kacame a tsakaninsu inda suka yi amfani da makamansu suka halaka juna
  • Al'amarin mai kama da almara ya faru ne yankin Rukenya da ke kusa da birnin Kutus a Kirinyaga da ke kasar Kenya

Reshe ya juye da mujiya a wani fashi da makami, yayin da wasu barayi suka samu sabani bayan wata sata da suka yi, wanda hakan ne yasa su yakar juna inda suka bar gawawwakin biyu a wani sannannen wuri cikin Rukenya kusa da birnin Kutus a Kirinyaga dake kasar Kenya.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

An tattaro yadda sama da 'yan fashi tara suka haura Thiba Falls Resort misalin karfe 3:00 na daren ranar Asabar, 19 ga watan Fabrairu, inda suka hanzarta yi wa mai gadin tsirara, gami da daure shi bayan sun nada mishi duka, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

'Yan fashi sun kacame da rikici suna tsaka da fashi, sun kashe junansu da makamansu
'Yan fashi sun kacame da rikici suna tsaka da fashi, sun kashe junansu da makamansu. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Baya ga haka, sun balle wata mashaya, inda suka yi tatul da giya kafin su diba wasu su dora kan abun hawan da suka aje wajen harabar.

Jim kadan, mambobin tawagar suka samu sabani inda suka fara yakar juna ta hanyar amfani da miyagun makamai, shafin Linda Ikeji ta ruwaito.

Mamallakin wurin sana'ar, Paul Kigundu ya isa wurin mintoci kadan bayan karfe 7:00 na safe bayan an sanar mishi da aukuwar lamarin.

"A lokacin da na isa, na tarar da jami'an 'yan sanda a wurin suna duba gawwakin biyu face-face cikin jini kwance wurin aje motoci. An samu fasassun kwalabe da yawa, wadanda ake zargin barayin sun yi amfani dasu wajen yakar juna," yace.

Kara karanta wannan

Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure aka ce yan bindiga sun tare hanya, Shehu Sani

Haka zalika, an samu miyagun makamai kusa da titi. Kwamandan 'yan sandan yankin gabacin Gichugu, Antony Mbogo, wanda ya halarci wurin, ya ki magana da manema labarai, sannan ya dage a kan cewa, ai suma manyan shi sun halarci wurin, yayin da yayi kokarin bayyana bayanan da suke a hannu, kafin ya kare da bayyana yadda lamarin ya auku.

Mutane da dama sun isa wurin don ganar wa idanun su gawawwakin dake kwance har karfe 9:00 na safe.

An kwashe gawawwakin daga wurin zuwa ma'adanar gawawwaki da ke asibitin Kerugoya mataki na 4, don ba wa 'yan sanda damar samun zanen yatsun su, saboda gano ko su waye yayin da aka kora masu cigaba da zuwan.

'Yan ta'adda sun toshe titin Yawuri zuwa Koko, sun sheke rai 3 a farmakin

A wani labari na daban, a ranar Asabar, 'yan bindiga sun tare titin birnin Yauri zuwa karamar hukumar Koko dake jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

Ganau daga birnin Yauri mai suna Umar Bachelor, ya shaida wa Vanguard ta waya yadda 'yan bindiga daga Rijau cikin jihar Neja suka tare titin birnin Yauri zuwa Koko, inda suka halaka a kalla mutane uku da ke taso daga jihar Neja zuwa Sakkwoto, a cewar sa 'yan bindigan sun sheke direba da mutane biyu.

Ya bayyana yadda lamarin ya dauki tsawon awa daya, ba tare da dakatarwa ba, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng