Soyayyar Facebook: Mata ƴar Indiya ta fasa auren masoyinta ɗan Najeriya a gaban mutane ranar ɗaurin aure
- Wata mata yar kasar Indiya ta fasa auren masoyinta dan Najeriya a ranar daurin aurensu bayan ta gayyace shi zuwa kasar su
- Kamar yadda bidiyon ranar auren ya nuna, matar wacce ta hadu da masoyinta a Facebook ta fice daga wurin daurin auren tana kuka
- A yayin da ta ke fice wa, an jiyo matar cikin hawaye tana cewa kai mutumin kirki ne kuma rayuwarka na tafiya lami lafiya
Wani mutum dan Najeriya ya shiga cikin damuwa bayan matar da zai aura ta yi watsi da shi a yayin da ake daf da daura musu aure, LIB ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a binrin Bangladesh kuma an gano cewa matan da mijin sun hadu ne a shafin dandalin sada zumunta na Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Daga bisani ne matar ta gayyaci saurayin dan Najeriya zuwa kasarta wato Indiya domin a daura musu aure.
An jiyo matar da ta fasa auren dan Najeriyan tana cewa, 'kai mutumin kirki ne kuma rayuwarka na tafiya lami lafiya' kafin ta fice daga wurin da za a daura musu aure tana kuka.
A cikin bidiyon an jiyo wata mata tana cewa 'church agbasala' (komai ya ruguje) a yayin da matar ke ficewa daga wurin daurin auren.
Ga dai bidiyon a kasa:
Martanin wasu 'yan Najeriya
@princexadewale ya ce:
"Idanun ta sun bude, komai ya tarwatse"
Shi kuma @Tradermmayne cewa ya yi:
"An samu matsala fa"
@AGOemmy ya ce:
"Haba kyakyawa, me yasa kika masa haka, babu wanda ba shi da aibu fa. Sai dai idan ba auren ki ke son yi ba. Ko kuma ki mayar da abin kasuwanci."
“Na Rasa Sukuni”: Dan Najeriya Ya Koka a Bidiyo, Ya ce Matar Da Ya Aura Ya Kai Turai Tana Sharholiya Da Maza
Ba zan iya ba: Jarabar mijina ta yi yawa, yana so ya kashe ni da saduwa, Matar aure ga kotu
A wani labarin, wata matar aure mai 'ya'ya uku, Olamide Lawal, a ranar Juma'a ta roki kotun Kwastamare da ke zamansa a Mapo, Ibadan, ya raba aure tsakaninta da mijinta, Saheed Lawal, saboda yana jarabar ta da yawan saduwa, rahoton Premium Times.
A karar da ta shigar, Olamide wacce ke zaune a Ibadan ta kuma yi ikirarin cewa mijinta ya saba shan giya ya yi tatil yana maye, The Nation ta ruwaito.
Ta ce:
"Mun shafe shekaru 14 muna zaman aure da Lawal. Tantirin mashayin giya ne kuma ba shi da tausayi ko kadan a zuciyarsa.
"Abin da ya mayar da hankali a kai shine shan giya, duka na da kuma tilasta min kwanciyar aure da shi. Baya kulawa da yaran mu.
"Ba zan iya cigaba da zama tare da shi ba."
Asali: Legit.ng