'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa

'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa

  • 'Yan crypto sun tafka asarar sama da Naira tiriliyan 1 yayin da farashin Bitcoin ya fadi zuwa kasa da $50,000 cikin sa'o'i 24 da suka gabata
  • A mafi karancinsa a ranar Asabar, Bitcoin daya ya nutse kasa da darajar $42,000, saukar da ta kai kasa har 22% cikin 100%
  • Faduwar dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar barazanar kwanakin kirsimati daga kasuwannin hannayen jari na duniya

'Yan crypto sun tafka babban faduwa a ranar Asabar bayan Bitcoin da wasu tsabobin intanet suka rage darajar sama da dala biliyan daya.

Wannan na faruwa ne yayin da 'yan crypto a duniya suka sayar da tsabobin kudaden intanet don daidaituwa da amintattun hannayen jari yayin da bukukuwan Kirsimeti ke gabatowa.

Kara karanta wannan

Yadda dukiyar Dangote ta kara yawa a 2021 fiye da ninkin yadda ya mallaka a baya

Kudaden intanet sun karye a duniya
'Yan crypto sun tafka mummunar asara yayin da darajar Bitcoin ta dungura kasa | Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Bitcoin shine mafi daraja a tsabobin kudaden intanet a daraja ta kasuwa, ya fado da 31.6% daga darajar $69,000 mafi girma a shekarar nan a ranar 10 ga Nuwamba.

Dangane da bayanai da aka tattaro daga CoinDesk, kafa mai darajar hannayen jari na kusan dala biliyan 900, ta nuna ana cinikin Bitcoin a farashi kasa da $42,000.

Bisa ga bayanai daga CoinMarketCap a lokacin rubuta wannan labarin, farashin Bitcoin ya kai $47,664.16.

Ethereum, wanda shi ne na biyu mafi daraja a kasuwannin kudaden intanet, shi ma ya fadi zuwa kasa da $3,905 a ranar, inda ya ragu da kusan 15% cikin 100%.

A lokacin hada wannan rahoton, kudin intanet na Altcoin ya karu inda ya tsaya a darajar $3,946.76 kowane daya. Duk da haka shi ma ya ragu da 13.46% a cikin awanni 24 da suka gabata da kuma 5.18% cikin 100% a cikin kwanaki bakwai da suka gabata.

Kara karanta wannan

Dalla-dalla: Yadda gidajen marayu za su cike fom din tallafin marayu na mawaki Davido

Me yasa Bitcoin ya fadi?

Kamar yadda rahoton Reuters ya ruwaito, faduwan wani sakamako ne na hasashe mai hadari tsakanin 'yan crypto wanda ya biyo bayan gano sabon nau'in Korona na Omicron.

Rahoton ya kuma nuna cewa ana iya danganta lamarin da wani batu na kwatsam da shugaban babban bankin Amurka Jerome Powell ya yi.

Kudin Intanet: Babban Bankin Najeriya CBN ya haramta kasuwancin Bitcoin

A tun farko a Najeriya, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya baiwa bankunan Najeriya umarnin rufe asusun 'yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kudaden intanet, matakin da bai yi wa dubban 'yan Najeriya dadi ba.

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma'a ga bankunan hada-hadar kudi (DMB) da kamfanonin da ba na harkar kudi ba (NBFI) da kuma sauran ma'aikatun harkokin kudi a kasar.

A cewar umarnin:

"Kari a kan umarnin da aka bayar tun a baya, bankin (CBN) yana tunatar da ma'aikatun da ke mu'amala da kudaden yanar gizo ko kuma dillancinsu cewa haramun ne."

Kara karanta wannan

Litar man fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi - ‘Yan kasuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.