Farashin man fetur: Kasashen Afrika 10 da suka fi Najeriya tsadar man fetur

Farashin man fetur: Kasashen Afrika 10 da suka fi Najeriya tsadar man fetur

A makon nan ne gwamnatin Najeriya ta bayyana yiyuwar cire tallafin man fetur a shekara mai zuwa, duba da yawan kudaden da gwamnatin ke kashewa wajen samar 'yan kasa mai.

Lamarin ya haifar da cece-kuce daga 'yan Najeriya, inda miliyoyin 'yan kasar suka bayyana rashin jin dadinsu ga wannan yunkuri.

Domin rage wa talakawa radadin cire tallafin, gwamnati tace za ta ware wasu kudade domin ba 'yan Najeriya alawus na zirga-zirga wanda ya Kai N5000 a duk wata.

Farashin man fetur a Afrika
Bincike: Farashin man fetur a wasu kasashen Afrika 10, Najeriya an fi arahar mai | Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Sai dai, cire tallafin zai iya cilla farashin man fetur daga N165 zuwa N340 ko fiye da haka, wanda hakan ka iya zama barazana ga jin dadin 'yan kasa.

A bangare guda, idan muka duba, Najeriya na daga cikin kasashen Afrika masu sayar da man fetur a kan farashin mai rahusa, ko da kuwa ya koma sama da N300.

Kara karanta wannan

Bankin Afrika zai ba Gwamna Ganduje Dala miliyan 110 domin ayi ayyuka a kauyukan Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani rahoton da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar TheCable, an tattaro wasu kasashen Afrika tare da bayyana farashin da suke sayar da man fetur.

Jerin kasashen Afrika da farashinsu na man fetur

1. Habasha - N225.16

2. Togo - N357.30

3. Mozambique - 444.98

4. Kenya - N482.03

5. Uganda - N529.36

6. Masar - 242.04

7. Benin - N368

8. Ghana - 482.03

9. Afrika ta Kudu - N498.08

10. Morocco - N534.72

Wannan kenan daga wasu kasashen Afrika guda 10, wanda a halin yanzu duka Najeriya ta fi su arahar man fetur, kamar yadda bincike ya bayyana.

Manyan wahalhalu 5 da 'yan Najeriya za su shiga idan man fetur ya koma N340, Shehu Sani

A sharhinsa, Sanata Shehu Sani, tsohon sanata daga jihar Kaduna, ya yi magana kan abubuwan da ‘yan Najeriya za su fuskanta idan farashin man fetur ya koma Naira 340 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Kalaman Sani sun biyo bayan sanarwar da Babban Manajin Darakta kuma Babban Jami’in NNPC ya yi cewa farashin man fetur na iya cillawa zuwa N320 ko N340 kan kowace lita bayan cire tallafin a shekarar 2022.

Da yake magana a shafinsa na Facebook, tsohon Sanatan ya bayyana abin da zai faru na kunci idan aka fara sayar da fetur a farashi mai tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.