Wata mata mai shekaru 40 da ta haifawa mijinta 'ya'ya 44 tace ya gudu ya barsu

Wata mata mai shekaru 40 da ta haifawa mijinta 'ya'ya 44 tace ya gudu ya barsu

  • Wata mata a nahiyarmu ta Afirka ‘yar shekara 40 ta haifi zunzurtun ‘ya’ya 44 tare da mijinta a tsawon rayuwarsu tare
  • Matar 'yar kasar Uganda ta haifi maza 22 da 'yan mata 16 tare da haihuwar da ta yi na karshe a watan Disamba 2016.
  • Matar da aka fi sani da Mama Uganda, ita ke kula da yaran da kanta yayin da mijinta ya yi sama da fadi da kudadensu

Uganda - Ba tare da samun wadataccen kulawar likita na musamman ba, wata mata mai suna Mama Uganda ta haifi yara 44 a tarayyarta da mijinta.

Matar da ta fito daga kasar Uganda ta fara haihuwa tun tana ‘yar shekara 13 bayan da iyayenta suka aurar da ita tana da shekara 12.

Hotunan mama Uganda da 'ya'yanta
Abin al'ajabi: Bidiyon wata mata mai shekaru 40 da ta haifi 'ya'ya 44 a tarayyar ta da mijinta
Asali: UGC

Mijinta ya cika wandonsa da iska

Kara karanta wannan

'Dan sanda ya gano matarsa na faɗa wa samarinta bata da aure, ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita

A cikin wani faifan bidiyo da wani mutum Joe Hattab ya yada a Facebook, matar mai shekaru 40 ta bayyana cewa ita uwa ce mara aure bayan mijinta ya yi watsi da su yayin da ya cika wandonsa da iska da kudadensu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar a yanzu haka ita ke daukar dawainiyar yaranta har 38 gaba dayansu - 6 daga cikinsu sun mutu.

Wani Balarabe mai halin kirki ne ya samar musu da gadajen da 'ya'yanta ke kwana akai amma Mama Uganda duk da haka ta samu damar sanya 'ya'yanta duka a makaranta.

Sau daya ta taba haifar da guda daya

Cikin murmushi mai fara'a, matar mai karfin hali ta bayyana cewa likitoci sun gaya mata cewa tana da tsarin haihuwa da akai-akai kuma hakan ya taimaka mata wajen yawan haihuwa.

Abin ban sha'awa a labarinta, ta haifi da guda daya sau daya ne kacal, duk sauran sun kasance tagwaye, 'yan uku da 'yan hudu.

Kara karanta wannan

Matar aure: Abin da yasa na yi garkuwa da kai na, na nemi miji na ya biya N50,000

Mama Uganda tana yara maza 22 da mata 16 wadanda har yanzu suna raye. Jimlar haihuwarta 44 sun kasance tagwaye sau 4, 'yan uku sau 5 da 'yan hudu sau 5 baya ga da daya da ta haifa.

An ba da rahoton cewa babu wata hanyar kayyade iyali da ta yi mata aiki a rayuwarta.

Hattab ya ziyarci gidan matar kuma ya yada bidiyon yadda cikin gidan yake.

Kalli bidiyon:

Martanin mutane a kafar sada zumunta

Ify Mado ya ce:

"Hakika ita jaruma ce, yakamata ta shiga kundin Guinness, baya ga haka, ya kamata shugaban kasar Uganda ya karbi ragamar kula da jin dadin iyalin baki daya. Dole ne ya shiga tarihi domin Allah ne kadai zai iya yin hakan. A tarihin kasar Uganda tabbas za a ambace ta, wannan abu ne da ba kasafai ba ake samu a duniya. Ina taya ki murna, Allah ya ci gaba da arzurta iyalanki."

Kara karanta wannan

Ruwan kudi: Bidiyon yadda wasu mutane suke ta kwasar kudade a kan titi a Amurka

Natasha Ibrahim ya rubuta:

"Allah ya albarkace ta ita da 'ya'yanta, da kyar zan iya kaiwa da cikina na da daya, Na so hakan da ganin shagalin da a kullum ke jiranta a gida. Irin wannan albarka haka."

Mary-Anne Delaney tayi tunani:

"Tana da kyau sosai, 'ya'yanta suna cikin farin ciki. Duk da haka, suna bukatar su sami taimakon kudi. Ya kamata dokokin su canza game da auren wuri. Allah ya albarkaci iyalinsu."

Matar da ta haifi yara 9 a lokaci guda ta magantu, ta ce suna sa ‘pampers’ 100 da shan madara lita 6 a kullum

A wani labarin, wata mata 'yar kasar Mali da ta haifi yara tara a lokaci guda a ranar 5 ga watan Mayu, 2021, a kasar Maroko, ta bayyana cewa yaran suna amfani da ‘pampers’guda 100 a rana guda.

Halima Cisse, wacce ta haifi yaran a cikin asibitin Casablanca, ta shaida wa Daily Mail cewa jariran na shan lita shida na madara a kowace rana.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Daga ƙarshe, Manchester United ta kori Ole Solskjaer

A cewar matar mai shekaru 26, wacce a yanzu haka tana da ‘ya’ya goma, ta yi matukar kaduwa bayan ta haifi yaran guda tara, maza hudu da mata biyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.