Kamar Idris Deby na Chadi, Firam Ministan Habasha, Abiy Ahmed, ya shiga faggen yaki da yan tawaye

Kamar Idris Deby na Chadi, Firam Ministan Habasha, Abiy Ahmed, ya shiga faggen yaki da yan tawaye

  • Firam Ministan Habasha ya cika alkawarinsa na daukar makami tare da shiga faggen fama don yakan Mayakan tawaye na Tigray
  • A baya, firaministan Habasha ya bukaci 'yan kasa da su dauki makamai domin kare kansu
  • Mataimakin Firam MInistan ne zai zama mukaddashin Shugaba kafin dawowar maigidansa daga faggen yaki

Addis Ababa - Firam Ministan kasar Habasha, Abiy Ahmad, ya jagoranci rundunar Sojojin kasarsa wajen yaki da yan tawayen Tigray da suka addabi gwamnatinsa, tashar yada labaran kasar ta sanar.

Tashar Fana a ruwaito ranar Laraba cewa Mataimakin Firam Minista, Demeke Mekonnen Hassen, zai rike ragamar mulki yanzu.

Kakakin Gwamnatin, Legesse Tulu, ya yi bayanin mika ragamar mulki ga mataimakin Abiy a hira da manema labarai, rahoton Fana.

Firam Ministan Habasha, Abiy Ahmed
Kaman Idris Deby na Chadi, Firam Ministan Habasha, Abiy Ahmed, ya shiga faggen yaki da yan tawaye Hoto: Ethiopia
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Read also

Shekih Ahmad Gumi ya sake jagorantar tawagar Malamai da Likitoci zuwa wani daji a jihar Kogi

Firam Ministan Habasha ya lashi takobin jagorantar rundunar Soji

A ranar Litinin, Abiy Ahmed ya sanar da cewa yana shirin shiga faggen fama da kasan domin yakar yan tawayen Tigray da abokansu.

A jawabinsa, ya yi kira garesu su hadu a faggen fama.

Yace:

"Mu hadu a faggen fama. Lokaci ya zo da zamu jagoranci kasar tare da sadaukar da kanmu."

Yan tawaye sun kewaye Addis Ababa, firaminista ya ce kowa ya dauki makami

A farkon watan Nuwamba, rahotanni sun ce 'yan kasar Habasha, 'yan kasashen waje da jami'an diflomasiyya na ficewa daga Addis Ababa yayin da dakarun 'yan tawaye suka kutsa cikin babban birnin kasar.

An ce mayakan Tigray da 'yan tawayen Oromo sun kewaye babban birnin kasar.

Rahoton Reuters ya ce, kasar Habasha ta kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni shida a ranar Talata bayan da ‘yan tawayen Tigray suka kwace wasu muhimman biranen kasar, inda suka ce sun nufi Addis Ababa babban birnin kasar.

Read also

Babu wanda aka kashe a Lekki Toll Gate: Lai Mohammed ya yi watsi da rahoton kwamitin EndSARS

Sanarwar ta zo ne kwanaki biyu bayan Abiy Ahmed, firaministan kasar, ya bukaci 'yan kasar da su dauki makami domin kare kansu daga jam'iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF).

Source: Legit Newspaper

Online view pixel