A mayar da Najeriya cikin jerin masu tauye 'yancin addini, hukuma a Amurka ga Biden

A mayar da Najeriya cikin jerin masu tauye 'yancin addini, hukuma a Amurka ga Biden

  • Hukumar da ke kula da 'yancin addini ta duniya, ta yi watsi da fitar da Najeriya daga cikin jerin masu take hakkin addini
  • Hukumar ta USCIRF ta ce matakin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dauka na cire Najeriya daga cikin jerin ya sabawa rahotonta na shekarar 2020
  • Hukumar wadda ta nuna rashin jin dadin ta game da kudurin ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta sake duba ta mayar da Najeriya cikin jerin sunayen

Hukumar kare 'yancin addinai ta Amurka USCIRF ta nuna adawa da cire Najeriya daga cikin jerin masu tauye 'yancin addini a fadin duniya.

A cewar USCIRF, Ma'aikatar Harkokin Wajen ba ta bi shawarar da ta bayar ba ta ayyana Najeriya a matsayin kasar mayar da hankali ta musamman (CPC) ba amma kawai ta sanya mata lakabi a matsayin kasar da ba ta da wani mummunan cin zarafin addini, in ji PM News.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: FG ta gargadi kungiyoyin kwadago ma'aikata kan amfani da kungiya ana karya doka

A mayar da Najeriya cikin jerin masu tauye 'yancin addini, hukuma a Amurka ga Biden
Kungiyar ta USCIRF ta yi kira ga gwamnatin Amurka da ta mai sake duba matakin cire Najeriya a jerin masu tauye hakkin addini (Hoto: Aso Rock Villa)
Asali: Twitter

Shugabar Hukumar ta USCIRF, Nadine Maenza, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 17 ga watan Nuwamba, ta ce hukumar ta ji takaicin matakin da gwamnatin Amurka ta dauka.

Don haka hukumar ta yi kira ga ma’aikatar harkokin wajen kasar da ta sake nazari tare da yin aiki da hujjojin da aka bayyana a cikin rahotonta na shekarar 2020.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Maenza ya ce:

“USCIRF ta ji takaicin cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen ba ta yi amfani da shawarwarinmu ba wajen zayyana kasashen da suka fi cin zarafin addini.
“Yayin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta dauki matakai kan wasu wuraren, USCIRF ta nuna rashin jin dadin yadda aka cire Najeriya daga jerin CPC, inda aka sanya ta a shekarar da ta gabata, tare da kawar ta Indiya, Syria da Vietnam.
"Muna kira ga Ma'aikatar Harkokin Wajen da ta sake nazarin sunayen ta bisa ga gaskiyar da aka gabatar a cikin rahotonta."

Kara karanta wannan

2022: Kano ta ware miliyan N800 domin magance talauci da rashin aiki a tsakanin mata

Amurka ta cire Nigeria cikin jerin kasashe masu tauye 'yancin addini

A wani labarin, kasar Amurka ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashen da ta ce suna tauye 'yancin masu yin addini a kasashensu, jaridar The Cable ta ruwaito.

Amurkan ta saka China, Rasha da wasu kasashe takwas a jerin kasashen da ta ce suna amfani da karfin iko wurin tauye hakkokin masu addini.

Sakataren Amurka Antony Blinken ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar mai taken 'Religious Freedom Designations'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.