An samu fashewar bama-bamai biyu a Kampala, babban birnin kasar Uganda
- An samu afkuwar fashe-fashen bama-bamai a babban birnin Kampala na kasar Uganda, wata kasa a Afrika
- Rahoto ya bayyana cewa, a halin yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba, amma an samu wadanda suka jikkata sama da 20
- Rahotannin da muka tattaro sun bayyana cewa, fashe-fashen sun faru ne da safiyar yau Talata 16 ga watan Nuwamba
Kampala, UgandaAn ji fashewar wasu bama-bamai biyu a birnin Kampala, babban birnin kasar Uganda.
Wani Derby Awio, mazaunin Kampala ne ya tabbatar wa jaridar TheCable faruwar lamarin da safiyar yau Talata.
Awio yace:
"Ba ma cikin kwanciyar hankali a Kampala."
An ce duka fashe-fashen biyu sun faru ne a tsakiyar birnin Kampala.
Yayin da daya ya tashi a kusa da ofishin 'yan sanda, an ce dayan ya faru ne a kusa da majalisar kasar.
Har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka mutu ba, amma an ce sama da mutane 20 sun jikkata.
NTV Uganda, wani gidan talabijin a kasar ya bayyana cewa:
"Ya zuwa yanzu an sami wadanda suka ji raunuka 27, bakwai daga cikin wadannan suna cikin mawuyacin hali - ma'aikatan lafiya na asibitin Mulago."
A rahoton AlJazeera, Emmanuel Ainebyona, kakakin ma'aikatar lafiya ta kasar, ya bayyana a wani sakon da ya wallafa cewa, an kwantar da mutane akalla 24 da suka samu raunuka sakamakon fashewar bama-bamai. Hudu daga cikinsu sun samu munanan raunuka.
Wani dan jarida a kafar yada labarai ta NTV a Uganda, ya ce ya ga guntun naman mutum a warwatse a kan titi.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
A watan da ya gabata, mutane biyu, ciki har da wata mace, sun mutu a wani harin da kungiyar ISIL (ISIS) ta dauki alhakin kaiwa.
Har ila yau, a watan da ya gabata, 'yan sandan Uganda sun ce wani dan kunar bakin wake ya tada bam a cikin wata motar bas, inda ya kashe kansa tare da jikkata wasu.
Harin ISWAP: Lamari ya yi zafi, sojoji sun sanya dokar hana fita a yankin Borno
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta kafa dokar hana fita a garin Askira Uba da kewaye a jihar Borno yayin da sojojin ke aikin dakile harin da aka kai a yankin.
A cewar PRNigeria, an tattaro cewa mayakan na ISWAP sun kaddamar da farmaki a Dille wanda cikin gaggawa sojoji suka dakile shi sakamakon hadin gwiwar dakarun sojin sama da na kasa.
Dille kauye ne a garin Lassa da ke karkashin karamar hukumar Askira Uba.
Asali: Legit.ng