Yaron Marigayi Muammar Gaddafi ya fito neman kujerar Shugaban kasa a zaben Libya
- Saif al-Islam Gaddafi ya yi rajista a matsayin ‘dan takara a zaben shugaban kasa da za ayi a Libya
- A ranar Lahadi hukumar zaben kasar Libya ta tabbatar da cewa Saif al-Islam ya shiga takarar 2021
- Yaron tsohon shugaban kasar zai fuskanci kalubale daga Firayim Minista, Abduk Hamid Dbeibah
Libya - Saif al-Islam Gaddafi ya bayyana shirinsa na neman takarar shugaban kasa a Libya. Aljazeera ta fitar da wannan rahoton a ranar Lahadin nan.
Rahoton yace daya daga cikin ‘ya ‘yan na Marigayi Muammar Gaddafi zai jarrabar sa’arsa a zaben shugaban kasan da za ayi a watan Disamban shekarar nan.
Hukumar zabe ta tabbatar da wannan, tace Saif al-Islam al-Gaddafi ya shiga cikin masu neman takara.
“Saif al-Islam al-Gaddafi ya gabatar da takardunsa ga hukumar zabe a garin Sebha… zai yi takarar shugaban kasa.” – Hukumar zabe ta kasar Libya.
Su wanene sauran 'yan takarar?
Sauran masu harin kujerar shugaban na Libya sun hada da Khalifa Haftar, Firayim Minista, Abdul Hamid Dbeibah da kuma shugaban majalisa, Aguila Saleh.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayan shekara da shekaru yana boye, ‘dan shugaba Muammar Gaddafi ya yi rajista a matsayin ‘dan takara a zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar bana.
BBC tace an ga Saif al-Islam Gaddafi cike da furfura, sanye da tabarau a cikin kayan gargajiya, yana rataye da rawani, ya na sa hannu a ofishin hukumar zabe.
Saif Al Islam Gaddafi yace yana so ya dawo da zaman lafiya a kasar Libya, bayan rikicin da ya barke tun bayan da aka hambarar da gwamnatin mahaifinsa.
Saif al-Islam zai kai labari a 2021?
Wani masani a cibiyar Doha, Farfesa Ibrahim Fraihat ya yi magana a kan zaben, yace Saif al-Islam Gaddafi yana da goyon-bayan wasu na-kusa da mahaifinsa.
Fraihat ya kuma bayyana cewa akwai wasu kabilun da suke son Saif al-Islam, amma duk da haka, bai yi karfin da zai iya lashe zaben shugaban kasa ba tukuna.
Babu mamaki Saif Al Islam Gaddafi ya fara shiri ne, amma ba dole ba ne ayi zaben a karshen bana.
Boko Haram a Najeriya
Har yanzu Boko Haram suna rike da wasu yankuna a Najeriya, inda aka ji Dakarun ISWAP sun sa wa direbobi da manoma haraji domin an zauna lafiya a Damboa.
Rahotanni sun ce sojojin ISWAP sun sha ban-ban da mayakan Abubakar Shekau da suke kashe mutane. Dakarun ISWAP suna karbar zakkah a hannun mutane.
Asali: Legit.ng