Habasha: 'Yan tawaye sun kewaye Addis Ababa, firaminista ya ce kowa ya dauki makami

Habasha: 'Yan tawaye sun kewaye Addis Ababa, firaminista ya ce kowa ya dauki makami

  • Mayakan tawaye na Tigray sun tunkari babban birnin kasar Habasha, Addis Ababa a makon nan
  • Tuni an sanya dokar ta baci domin tabbatar da tsaro da dawowar lamura zuwa yadda suke a baya
  • Hakazalika, firaministan Habasha ya bukaci 'yan kasa da su dauki makamai domin kare kansu

Habasha - An ce 'yan kasar Habasha, 'yan kasashen waje da jami'an diflomasiyya na ficewa daga Addis Ababa yayin da dakarun 'yan tawaye suka kutsa cikin babban birnin kasar.

An ce mayakan Tigray da 'yan tawayen Oromo sun kewaye babban birnin kasar, TheCable ta ruwaito.

Da dumi-dumi: 'Yan Habasha sun fara tserewa daga Addis Ababa yayin da 'yan tawaye ke shigowa
'Yan tawaye sun tinkari Addis Ababa | Hoto: aljazeera.com
Asali: Depositphotos

Rahoton Reuters ya ce, kasar Habasha ta kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni shida a ranar Talata bayan da ‘yan tawayen Tigray suka kwace wasu muhimman biranen kasar, inda suka ce sun nufi Addis Ababa babban birnin kasar.

Kara karanta wannan

Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa

Sanarwar ta zo ne kwanaki biyu bayan Abiy Ahmed, firaministan kasar, ya bukaci 'yan kasar da su dauki makami domin kare kansu daga jam'iyyar Tigray People's Liberation Front (TPLF).

An ce Ahmed ya bukaci 'yan kasarsa da su "dauki makamai su kare" a Addis Ababa daga 'yan tawaye.

A cewarsa:

“A dauki duk wani nau’in makamin da za a iya tunkarar kungiyar ta TPLF mai barna da shi, a kifar da ita a binne ta. Mutuwa don Habasha ya zama wajibi (ga) mu duka."

A ranar 2 ga watan Nuwamba, Amurka ta ba da shawarar yin balaguro, tana mai cewa yanayin tsaro a Habasha ya tabarbare matuka a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, sakamakon ci gaba da tashe-tashen hankulan da ake fama da su a yankunan Amhara, Afar da kuma Tigray.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An bindige wani mutum a kotu yayin da ya yi ƙoƙarin tseratar da fursuna

Sanarwar ta kara da cewa:

"Babban kaso na babbar hanyar A2 da ta hada Addis Ababa da birane zuwa arewa hukumomin tarayya sun hana binsu, lamarin ya haifar da tarzoma, makalewar matafiya, da kuma yanayin balaguron mai muni."

An damke Sojoji 40 da sukayi kokarin juyin mulki a kasar Sudan

A wani labarin, wasu jami'an Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki ranar Talata kuma an damke yawancin Sojojin, a cewar wasu manyan jami'an gwamnatin kasar da Sojoji ga tashar CNN.

An damke kimanin Sojoji 40 da sukayi kokarin kwace gidan talabijin da hedkwatar Sojojin kasar, wani babban jami'in kasar da aka sakaye sunansa ya fada.

Bayan rashin nasarar da aka yi na juyin mulki, an baza jami'an tsaro cikin birnin Khartoum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.