Aisha Ahmad
1219 articles published since 27 Mar 2024
1219 articles published since 27 Mar 2024
Bayan shafe kwanaki 15 a hannun masu garkuwa da mutane, yaran mai Shari'a Janet Galadima sun shaki iskar 'yanci. Yanzu haka yaran na tare da mahaifiyarsu.
Shugaban jami'ar Dutsin-ma a jihar Katsina (FUDMA), Farfesa Armaya'u Bichi ya zargi wasu ma'aikatan jami'ar da aiki da 'yan ta'adda ta hanyar ba su bayanai.
Biyo bayan koken jama'ar Liberia kan matsin tattalin arziki, shugaban kasar, Joseph Boakai ya ragewa kansa albashi saboda matsin da yan kasar ke fuskanta.
Rundunar yan sandan Kano ta damke matashi mai shekaru 22 Zakariyya Muhammad da zargin sace yar makocinsa mai shekaru biyu da rabi a duniya,tare da neman fansa.
Hukumar kula da yawon bude idanu a jihar Plateau ta bayyana cewa Kura ta tsere daga gidan adana namun daji na Jos, inda aka nemi jama'a su sa ido.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta sanya ranar 17 Yuli, 2024 domin yanke hukunci ka bukatar tsohon gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele.
Gwamnatin tarayya ta amince da shigo da wasu muhimman kayan abinci ba tare da biyan kuɗin haraji ba, kamar yadda Ministan noma, Abubakar Khadi ya sanar a Abuja.
Matasa a jihar Kano sun fara barranta kansu da duk wani yunkuri na marawa auren jinsi da dangoginsa baya a kasar nan, inda su ka gudanar da zanga-zanga a yau.
Hukumar Hisbah ta nesanta kanta da gayyatar kungiyar da aka gano ta na cusa ra'ayin auren jinsi da dangoginsa 'WISE' a Kano, inda ta ce ba ta san jami'in ya je ba.
Aisha Ahmad
Samu kari