Bayan shekaru 5 ana shari'a, an bawa masallaci ikon cigaba da kiran sallah a Jamus

Bayan shekaru 5 ana shari'a, an bawa masallaci ikon cigaba da kiran sallah a Jamus

- Kotu a kasar Jamus ta bawa musulmin wani gari damar cigaba da kiran sallah a wani masallaci bayan hana su na shekaru biyar

- Wasu ma'aurata ne da ke zaune mita 900 daga masallacin suka shigar da kara kan cewa kiran sallar yana shiga hakkinsu

- Sai dai kotun da ke Muenster ta yi watsi da wannan karar inda ta ce kowa na da ikon yin addinsa muddin bai tilastawa wani yin addinin ba

DUBA WANNAN: APC ta dakatar da hadimin Buhari, surukin Tinubu da wasu mutane takwas

Bayan shekara 5 an halastawa masallaci cigaba da kiran Sallah Jamus
Bayan shekara 5 an halastawa masallaci cigaba da kiran Sallah Jamus
Asali: Twitter

Wata kotu a Jamus a ranar Laraba ta yi watsi da karar da aka shigar na hana kiran sallah a wani masallaci da ke wani karamin gari bayan shekaru biyar ana kai ruwa rana a kan batun.

Musulmin garin Ditib (galibinsu 'yan Turkiyya) yanzu za su iya cigaba da amfani da na'urar amsa kuwa wurin kiran sallah a garin Oer-Erkenschwick da ke Arewacin Rhine-Westphalia.

Mazauna garin sun shigar da kara a 2015 a kan damar da aka bawa masallacin na amfani da na'urar amsa kuwa na a kalla mintuna 15 daga karfe 12 zuwa 2 na rana a ranakun Juma'a.

KU KARANTA: Za mu kafa kasar Yarabawa ba tare da tada fitina ba - Farfesa Akintoye

An kashe shekaru 5 ba a kirar salla a garin saboda karar da wasu ma'aurata da ke zaune mita 900 daga masallacin suka shigar inda suka ce kirar sallar yana shiga hakkinsu na yin addininsu.

Kotun da ke zamanta a Muenster ta yi watsi da hujjar da suka gabatar.

"Dole kowa ya amince cewa sauran mutane suna da ikon yin addininsu," a cewar mai shari'a Annette Kleinschnittger

Tunda dai ba su tilastawa kowa yin addininsu ba, babu dalilin da za ayi korafi a kai, a cewar mai shari'ar.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis.

Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel