'Yan bindiga sun sace ƴan gida ɗaya su takwas a Abuja

'Yan bindiga sun sace ƴan gida ɗaya su takwas a Abuja

Wasu mutane dauke da bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan tsohon direktan hukumar kananan hukumomi, ACSC, Alhaji Attahiru Abdullahi Pandagi, da ke Agyana road, Abaji, suka sace ƴaƴansa takwas.

Daily Trust ta ruwaito cewa wadanda aka sace sun hada da Jibrin, 26; Bashir, 24; Jamilu 26; Abdullahi 24; Abdulrahman 25; Abubakar 23; Muazu 22 da Isah, 12.

Majiyar Legit.ng ta ruwaiti cewa yan bindigan sun raba kansu kashi uku ne suka kai wasu hare haren a lokaci guda a Angwar Sabon Tasha da wani mashaya da ke kallon ofishin FRSC a unguwar.

An sace ƴan gida ɗaya su takwas a Abuja
An sace ƴan gida ɗaya su takwas a Abuja. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Mahaifiyin yaran, Alhaji Attahiru Abdullahi Pandagi yayin zantawa da majiyar Legit.ng ya ce wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen sun haura katanga yayin da wasu suka tare wasu hanyoyin shiga gidan.

DUBA WANNAN: An haifi jariri rike da na'urar hana haihuwa a hannunsa (Hotuna)

Ya ce 'yan bindigan sun shiga dakunan samari inda yaran ke barci sun taso keyarsu da bindiga duk da cewa ya ce baya gida a lokacin da abin ya faru.

Ya ce, "Daya daga cikinsu ya tambayi matata cewa ina Isah ya ke, hakan ke nuna alama cewa suna da dan leken asiri da ya taimaka musu da bayanai."

An gano cewa wasu yan banga da ke gadin gidajen manyan maaikata a unguwar sunyi musayar wuta da masu garkuwa da mutanen hakan yasa suka tsere daga unguwar.

Wani na kusa da shugaban karamar hukumar, Alhaji Abdulrahman Ajiya, da ya nemi a sakaya sunansa ya ce shugaban ya shiga matukar damuwa saboda harin hakan yasa ya tafi Abuja ya shaidawa Minista abinda ya faru.

Ya ce, "Shugaban karamar hukuma ya damu sosai game da harin da masu garkuwa da mutane suka kawo, ya tafi Abuja domin ya sanar da minister abinda ya faru."

Idan ba a manta ba, wasu 'yan bindiga a farkon makon nan sun sace diyar wani jigo a jami'yyar APC, Mrs Hasiya Gimba Bako sun kuma nemi a biya su kudin fansa Naira Miliyan 2.

Da aka tuntube shi, Kakakin rundunar 'yan sandan Abuja, DSP Anjuguri Manza ya tabbatar da sace yaran inda ya ce ana kokarin ganin an ceto wadanda abin ya faru da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel