Budurwa ta auri dan ajinsu na sakandare bayan shekaru 17, hotunan kammala makarantansu a 2004

Budurwa ta auri dan ajinsu na sakandare bayan shekaru 17, hotunan kammala makarantansu a 2004

  • Wata matashiya ‘yar Najeriya ta raya Sunnah tare da dan ajinsu na makarantar sakandare bayan shekaru 17
  • Da take yada hotunansu na kammala makarantar sakandare a 2004, budurwar ta bayyana cewa koda dai sun kasance abokai tsawon shekaru 17, sun yi soyayya ne na dan lokaci kankani
  • Da take tuna labarin da ke tattare da hotunan kammala makarantar tasu, ta ce mai daukar hoton ya sanya su a tsakiya saboda kankantarsu a tsakanin abokan karansu a waccan lokacin

Soyayya ta yi halinta yayin da wata budurwa ‘yar Najeriya ta auri dan ajinsu na makarantar sakandare shekaru 17 bayan kamala karatunsu.

Amaryar wacce ke cike da farin ciki ta je shafinta na Instagram domin wallafa hotunansu na kammala makarantar sakandare a 2004 tare da hotunan aurensu na 2021.

Read also

Zamfara: A kalla rayuka 12 sun salwanta, 'yan bindiga sun kone motar 'yan sanda

Budurwa ta auri dan ajinsu na sakandare bayan shekaru 17, hotunan kammala makarantansu a 2004
Budurwa ta auri dan ajinsu na sakandare bayan shekaru 17, hotunan kammala makarantansu a 2004 Hoto: @funky_okboying
Source: Instagram

Sun kasance abokai tsawon shekaru 17

A cewar matashiyar, ita da masoyin nata sun kasance abokai tsawon shekaru 17 da suka gabata sannan sun yi soyayya ne na shekara daya kafin suka shiga daga ciki a 2021.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da take martani kan hotunan kammala karatunsu na sakandare a 2004, sabuwar amaryar ta ce mai daukar hoton ya sanya su a tsakiyar abokan karatunsu saboda kankantar jikinsu.

Ta ce mai daukar hoton bai san cewa yana shirya wani dan karamin aure bane a waccan lokacin.

‘Yan Najeriya sun yi martani

@t.i.w.a.l.o.l.a_____ ta ce:

"Awwwwn wannan yayi kyau dukka ‘yan ajinmu na makarantar sakandare sun zama ‘yan duniya da ‘yan yahoo.”

@t.m_albert ya rubuta:

"Ka auri abokinka babu abun da ya fi shi, Allah ya riga ya albarkaci wannan aure da fahimtar juna da tallafawa juna.”

Read also

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

@jerr_malik ya ce:

"Anita mu amma kika bar ni a zamanin makarantar firamare don kawai sun rubuta sunana cikin masu surutu kuma sunana ya bayyana sau biyu.”

Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

A wani labarin, wani mutumi ya nemi a kawo karshen aurensa da masoyiyar matarsa saboda kazama ce bata wanka kullum-kullum.

A rahoton Aminiya, matar ba ta ji daɗin wannan zance na mai gidanta ba, wanda suka kwashe shekariu biyu suna gina soyayyarsu bayan Aure.

Matar dake zaune a Uttar Pardesh na Kasar Indiya, ta yi gaggawar garzayawa zuwa wurin wata ƙungiyar dake fafutukar kare hakkin mata domin ta shiga cikin lamarin ta hana kudirin mijinta ya cika.

Source: Legit.ng

Online view pixel