Dan majalisa ya hango matsala, ya ce APC na kitsa magudi a zaben 2023
- An zargi jam’iyyar All Progressives Congress da kulla-kulla don yiwa duk sauran jam’iyyun siyasa magudi a zaben 2023
- Dan majalisar wakilai ne yayi wannan zargi a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba
- Honourable Ayo Yusuf ya ce akwai bukatar amfani da mataki na doka kan shugabancin majalisar dokokin kasar kan wannan al’amari
Abuja – Wani dan majalisar wakilai, Ayo Yusuf, a ranar Laraba, 13 ga watan Oktoba, ya yi zargin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na shirya wani tsari na yin magudio gabannin zaben 2023.
Yusuf ya ce akwai alamu da ke nuna cewa ana iya tunkarar jam’iyyar mai mulki don yanke hukunci kan takaitawa jam’iyyun siyasa yin amfani da zaben fidda gwani na kato-bayan-kato a gyaran fuskar da ake yiwa dokar zaben 2010.
Dan majalisar ya yi watsi da wannan shawara ta bai daya da majalisun dokokin kasar suka yanke na wajabta amfani da tsarin kato-bayan-kato ga mambobin jam’iyyun da ke neman kujerun shugabanci.
Yusuf ya ce wannan hukunci da majalisar dokokin tarayya ta yanke manufa ne na ganin shirin APC na magudin zabe ya tafi daidai.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake bayyana cewa ba a ba ‘yan majalisu musamman na jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) damar yin muhawara kan lamarin ba, Yusuf ya ce akwai bukatar daukar matakin doka kan majalisar.
Ya ce:
“Na kasance a zauren majalisar kuma nayi adawa da hakan amma ba a bari anyi muhawara ba.”
“Daya, baya daga cikin rahoton, ya zo ne a matsayin gyara kuma a wannan rana, na fada ma kakakin majalisa cewa kuskure ne; cewa kotun koli ta yanke hukunci – ba zan iya tuna bayanin shari’ar ba yanzu – cewa a bari jam’iyyu su yanke hukunci kan irin tsari da suke so wajen zabar yan takararsu.”
Ya yi gargadin cewa shugabancin Majalisar Dokoki ta kasa suna kwace hakkin jam’iyyun da ake sa ran za su tattauna a kan lamarin kuma ana iya kalubalantar su.
Ku yi magudi a zaben Anambra, ku mutu a hatsarin jirgin sama – Fasto ta gargadi ‘yan siyasa
A wani labarin, Shugabar Centre for Psychic and Healing Administration (CPHA), Flora Ilonzo ta shawarci 'yan siyasa da ke shirin yin magudi a zaben ranar 6 ga watan Nuwamba, a jihar Anambra da su manta da irin wannan tunani.
A cewarta, duk wanda ya yi magudi a zaben zai iya mutuwa mai radadi a hadarin jirgin sama.
Ta ce gargadin ya zama dole saboda kowa na bukatar sanin sakamakon irin wannan matakin, jaridar The Sun News ta rahoto.
Asali: Legit.ng