Hotunan mawaki Grand P yayin da ya ke bayyana kaunarsa ga rusheshiyar budurwarsa

Hotunan mawaki Grand P yayin da ya ke bayyana kaunarsa ga rusheshiyar budurwarsa

  • Fitaccen mawaki mai karamin jiki na kasar Guinea, Grand P ya wallafa hotunansa da zukekiyar budurwarsa kuma rusheshiya, Eudoxie Yao
  • Cike da kauna tare da shaukin soyayya, Grand P ya jera zafafan kalaman soyayya ga budurwarsa inda ya ce ba zai daina son ta ba
  • Kamar yadda ya sanar cikin kalaman soyayyar, ya na cikin farin cikin alakarsu kuma ya na fatan Ubangiji ya bai wa soyayyarsu kariya

Guinea - Hausawa kan ce soyayya gamon jini. Babu shakka hakan ta ke ballantana idan aka duba lamarin fitaccen mawakin kasar Guinea, Grand P da kuma zukekiyar budurwarsa 'yar asalin kasar Ivory Coast, Eudoxie Yao.

Duba da banbanci a girman jikin, mawakin dan tsurut ne amma budurwar ta sa shirgegiya ce, lamarin da yasa suka zama mutane biyu mabanbanta a bayyane.

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun sharia ta umurci a yi wa magidanci bulala 80 saboda yi wa matarsa ƙazafi kan haihuwar ɗansu na 6

Hotunan Grand P yayin da ya ke bayyana kaunarsa ga rusheshiyar budurwarsa
Hotunan Grand P yayin da ya ke bayyana kaunarsa ga rusheshiyar budurwarsa. Hoto daga Grand P
Asali: Facebook

Sai dai kuma da ya ke so gamon jini ne, sai ga shi mawakin ya wallafa hotunan shi da zukekiyar budurwarsa tare da kalamai masu dadi da tausasa zuciya.

A bayyane ya ke sanar da irin kaunar da ya ke mata tare da nuna yadda ya ke son ganin farin cikin ta.

Mawakin ya je shafinsa na Facebook a daren Juma'a, 8 ga watan Oktoba, inda ya wallafa hotonsa da Eudoxie tare da fatan Ubangiji ya bai wa soyayyarsu kariya.

A kalaman mawakin:

"Ina son ki kasance cikin farin ciki a kowanne minti da dakika. Ina kaunar ki sosai kuma ina farin cikin kasancewar ki a rayuwa ta. Ina fatan ki cigaba da kasancewa mai samar min da farinciki ya abar kauna ta," ya rubuta.

Kara karanta wannan

Buhari ya ce gwamnatinsa ta shirya za ta fara kera makamai saboda wasu dalilai

"Ke ce mafi girman mu'ujiza da ta taba faruwa da ni, mace mai matukar tsada, wacce na fi kauna. Ina son ki! Ina son ki! Ki saurari zuciya ta kuma ki kalle ni.
"Ba don ni ba, saboda mutunci na, na rantse zan yi miki biyayya. Babu abinda zai sauya kauna ta gare ki. Ubangiji ya kare soyayyarmu. Eudoxie Yao," ya kara da cewa.

Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure

A wani labari na daban, wani mutum daga kauyen Kwaramba a garin Gokwe na kasar Zimbabwe ya sha harbin kudajen zuma yayin da ya ke kwance turmi da tabarya da matar aure.

Kamar yadda LIB suka ruwaito, an tattaro cewa Jethro Maimba ya labe a daji inda ya kwanta da Lizzie Maphosa yayin da al'amarin ya faru.

Wani mazaunin kauyen da ya san yadda lamarin ya faru, ya sanar da B-Metro cewa kudajen zuman sun daina harbin Maimba ne bayan da ya roki yafiyar Musariri.

Kara karanta wannan

Shege talauci, ina fatan Ubangiji yayi min tsari da shi: Bidiyon Melaye a jirgin Orji Kalu

Asali: Legit.ng

Online view pixel