Shege talauci, ina fatan Ubangiji yayi min tsari da shi: Bidiyon Melaye a jirgin Orji Kalu

Shege talauci, ina fatan Ubangiji yayi min tsari da shi: Bidiyon Melaye a jirgin Orji Kalu

  • Wani bidiyon Sanata Dino Melaye a cikin jirgin Sanata Orji Kalu ya bayyana a cikin ranakun karshen makon nan
  • Cike da annashuwa Dino Melaye ke cewa bikin duniya da mai rai ake yi, ya yi addu'ar Ubangiji ya tsare su daga talauci
  • Dan siyasan bai iya boye farin cikinsa ba, cike da murna ya ce talauci shege ne, gara ya manta da matsalolinsa na wani lokaci

Sanata Dino Melaye a cikin ranakun karshen makon da ya gabata ya hau jirgin tsohon gwamnan jihar Abia kuma Sanata mai ci a yanzu, Sanata Orji Uzor Kalu.

Babu shakka tsohon sanatan ya kasa boye tsabar farin cikinsa da annashuwa yayin da ya ke cikin jirgin babban dan siyasan.

Bai yi kasa a guiwa ba, tsohon sanatan kuma fitaccen masoyin rayuwar jin dadin ya dinga addu'a tare da fatan Ubangiji ya tsare shi daga talauci.

Read also

Tunde Bakare ya yi magana game da shirin takarar 2023 bayan ya sa labule da Buhari

Shege talauci, ina fatan Ubangiji yayi min tsari da shi: Bidiyon Melaye a jirgin Orji Kalu
Shege talauci, ina fatan Ubangiji yayi min tsari da shi: Bidiyon Melaye a jirgin Orji Kalu. Hoto daga @dinomelaye
Source: Instagram

Kamar yadda shafin Linda Ikeji Blog ya wallafa a Instagram, an ga bidiyon sanatan tare da Orji Kalu suna shewa tare da annashuwa mara misaltuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Cike da jin dadin tare da nuna cewa rayuwa ta na gara masa yadda ya so, Melaye ya ce:

"Rayuwa nan ta yi. Bikin duniya da mai rai ake yi. Gara mu manta da matsalolinmu na dan wani lokaci. Talauci shege ne. Ina neman tsarin Ubangiji daga gare shi."

Dakarun sojojin Najeriya sun bindige 'yan awaren IPOB 3

A wani labari na daban, dakarun sashi na 5 na atisayen Golden Dawn da aka tura Enugu sun sheke mutum 3 da ake zargin 'yan awaren kudu ne da aka fi sani da IPOB, wadanda suka kai wa 'yan sanda farmaki kan babbar hanyar Okija zuwa Onitsha a ranar 7 ga watan Oktoba.

Read also

Mun yi amfani da aikin noma wajen tsamo sama da mutum milyan 4 daga Talauci, Ministan Noma

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, kamar yadda takardar da kakakin dakarun sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu ya fitar tace, zakakuran sojin sun yi artabu da miyagun kuma suka fi karfinsu, lamarin da yasa suka arce.

"Dakarun sojin ba su kakkauta ba suka bi su tare da cigaba da zuba musu ruwan wuta. Uku daga cikin 'yan bindigan da ke tuka motoci biyu kirar Hilux da Hummer bus ne suka bakunci lahira yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika."

Source: Legit.ng

Online view pixel