Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure

Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure

  • Alhaki ya kama wani mutum yayin da ya ke kwance turmi da tabarya da wata matar aure a wani daji a Zimbabwe
  • Kudajen zuma ne masu yawa suka dinga harbin Maimba yayin da ya ke tsaka da biyan bukatarsa da matar aure
  • Kwanaki biyu kudajen zuman suka kwashe suna harbinsa a gaba, har sai da ya roki mijin matar yafiya sannan suka watse

Zimbabwe - Wani mutum daga kauyen Kwaramba a garin Gokwe na kasar Zimbabwe ya sha harbin kudajen zuma yayin da ya ke kwance turmi da tabarya da matar aure.

Kamar yadda LIB suka ruwaito, an tattaro cewa Jethro Maimba ya labe a daji inda ya kwanta da Lizzie Maphosa yayin da al'amarin ya faru.

Kara karanta wannan

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Mijin Maphosa mai suna Joseph Musariri an gano cewa ya ja kunnen Maimba sau babu adadi kan ya daina kwanciya da matarsa. Daga nan ne ya yi tsinuwa kan matarsa wacce kuwa ta bi su.

Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure
Kudajen zuma sun dinga harbin wani mutum yayin da ya ke turmi da tabarya da matar aure. Hoto daga lindaikejiblog.com
Asali: UGC

Wani mazaunin kauyen da ya san yadda lamarin ya faru, ya sanar da B-Metro cewa kudajen zuman sun daina harbin Maimba ne bayan da ya roki yafiyar Musariri.

Mazaunin kauyen ya ce:

"Mun zargi cewa harbin zuman duk na asiri ne saboda wasu daga cikin kudajen zuman sun rufe gaban shi na kwanaki biyu.
"Kudajen zuman sun bace ne bayan Maimba ya roki gafarar Musariri. Wannan ya biyo bayan alkawarin da suka yi na cewa zai biya shi fansar dabbobi biyu".

Daga bisani an gano cewa Musariri da Maimba sun yi yarjejeniyar zuwa wurin babban alkalin kotun gargarjiyar yankin inda za su yi sasanci.

Kara karanta wannan

A tura matasan NYSC faggen yaki da yan bindiga, wanda ba zai je ba a daina biyansa albashi

A yayin da aka tuntubi Alkali Nemangwe, ya ki tabatar da aukuwar lamarin kuma bai musanta ba. Ya ce:

"Har yanzu ba a kawo mana lamarin gabanmu ba. Ta yuwu sun yanke shawarar sasanci a tsakaninsu.
"Sau da yawa ana kawo irin wannan lamarin gaba na ne bayan wadanda lamarin ya shafa sun kasa sasantawa."

Wata sabuwa: 'Yan awaren IPOB sun haramta cin 'Naman Shanun Fulani' a kudu maso gabas

A wani labari na daban, kungiyar masu son kafa kasar Biafra ta IPOB, ta haramta cin naman shanu a yankin kudu maso gabas, TheCable ta wallafa.

A wata takarda da aka fitar a ranar Asabar ta hannun Chika Edoziem, daraktan kungiyar, ya ce kungiyarsu ta ce wannan haramcin zai fara aiki a watan Afirilun 2022.

Kungiyar IPOB, wadanda suka dinga saka dokar zaman gida dole a yankin kudu maso gabas, ta ce wannan haramcin zai kawo karshen matsanancin harin da ake kai wa jama'a a yankin kudu maso gabas.

Kara karanta wannan

Ku ba 'yan bindiga hadin kai don tsira da rayukanku, shawarin 'yan sanda ga 'yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng