Karshen zamani: Mahaifi ya yi hayar 'yan daba su lakadawa malamin 'yarsa duka

Karshen zamani: Mahaifi ya yi hayar 'yan daba su lakadawa malamin 'yarsa duka

  • Rundunar 'yan sanda sun cafke wani mutum bisa laifin kai 'yan daba makarantar 'yarsa don su doki malami
  • Rahotanni sun bayyana cewa, malamin ya daki 'yar mutumin ne, lamarin da ya bata masa rai sosai
  • A halin yanzu mutumin da shi da 'yan daban suna hannun 'yan sanda ana ci gaba da bincike

Abeokuta, Ogun - Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 35, Abidemi Oluwaseun da laifin hayar 'yan daba don kai hari kan wani malami saboda ya lakadawa ‘yarsa mai shekaru 15 duka.

Rahotanni sun bayyana cewa Oluwaseun ya dira kwalejin 'yan mata ta Baptist dake Idi-Aba a Abeokuta tare da 'yan daba biyu a ranar Talata 12 ga watan Oktoba don tunkarar wani malamin da ya zarga da dukan 'yarsa.

Read also

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun sake kai hari jami'ar Arewa, Sun yi awon gaba da dalibai

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a cikin wata sanarwa, Punch ta ruwaito.

Karshen zamani: Mahaifi ya yi hayar 'yan daba su lakadawa malamin 'yarsa duka
Taswirar jihar Ogun| Hot: thenationonlineng.net
Source: Getty Images

Oyeyemi ya ce an cafke wanda ake zargin tare da wasu mutum biyu; Fayesele Olabanji mai shekaru 25, da Alebiosu Quawiyu mai shekaru 24.

Jami'in ya kara da cewa ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa ne daga shugaban makarantar.

Oyeyemi ya ce 'yan sanda sun yi nuni da cewa wasu mutane uku sun dira makarantar da motar da ba ta da rajista, dauke da sabbin adduna kuma suna barazanar yi wa malamin makarantar lalata.

Ya ce:

“Bayan kiran gaggawa, DPO, reshen Kemta, CSP Opebiyi Sunday, ya tattara mutanensa ya tafi wurin da aka kama mutanen uku a harabar makarantar. An kwato mota Toyota da ba a yi wa rajista ba da kuma adda.

Read also

An kashe manoma uku a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Filato

Yadda lamarin ya faru

Sanarwar da take bayyana yadda lamarin ya faru, Oyeyemi ya bayyana cewa:

“Malamin bayan ya gano wadanda ke tayar da hankali a aji ya yi musu bulala a matsayin ladabtarwa, amma 'yar wanda ake zargin ta tafi gida ta kai karar abin da ya biyo baya inda mahaifinta ya hada ‘yan daba guda biyu suka kutsa makarantar da adda.”

Oyeyemi duk da haka ya ce Kwamishinan ‘yan sanda, Lanre Bankole, ya ba da umarnin a binciki wadanda ake zargi da kyau kuma a gurfanar da su a kotu cikin gaggawa.

MURIC ta goyi bayan malamai suke ladabtar da dalibai a makarantun Islamiyya

A wani labarin, Shahararriyar kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta yi martani kan abin da ya faru da ta kira mara dadi na cin zarafin dalibai a wata makarantar Islamiyya a jihar Kwara.

MURIC ta nemi gwamnatin jihar da ta duba bidiyon da ake yadawa cikin tsanaki tare da bincikar lamarin yadda ya dace.

Read also

Tsoho mai shekaru 60 ya kashe ɗansa mai shekaru 32 saboda saɓani da ya shiga tsakaninsu

Kungiyar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin 11 ga watan Oktoba, wacce Legit.ng Hausa ta samo dauke da sa hannun shugaban na MURIC, Farfesa Ishaq Akintola.

Source: Legit

Online view pixel