EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami’a kan badakalar N260m

EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami’a kan badakalar N260m

  • Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban jami'ar tarayya ta Gusau
  • EFCC ta gurfanar da Farfesa Magaji Garba ne a gaban Mai shari'a Maryam Hassan kan laifin damfarar kudi har N260m daga wurin dan kwangila
  • Tsohon malamin makarantar ya dinga tatsar kudi daga hannun dan kwangila da zummar cewa za a bashi kwangilar N3b ta katangar makarantar

FCT, Abuja - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranar 12 ga watan Oktoban 2021 ta gurfanar da tsohon shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau, Farfesa Magaji Garba.

EFCC ta gurfanar da tsohon malamin makarantar ne a gaban Mai shari'a Maryan Hassan Aliyu ta babbar kotun tarayya da ke Jabi a Abuja.

Kara karanta wannan

Hotunan Osinbajo na gudu a filin motsa jiki yayin karbar bakuncin gasar Baton

EFCC ta gurfanar da shugaban jami’a kan badakalar N260m
EFCC ta gurfanar da shugaban jami’a kan badakalar N260m. Hoto daga Economic and Financial Crimes Commission
Asali: Facebook

Kamar yadda hukumar ta bayyana, ana zarginsa ne da laifuka biyar da suka hada da samun kudi ta hanyar karya, damfara tare da takardun jabu.

An zargi cewa ya tatsi kudi masu yawa daga dan kwangila inda ya fake da cewa zai ba shi kwangilar yin katangar da za ta zagaye dukkan jami'ar kan kudi naira biliyan uku.

Kamar yadda EFCC ta wallafa a shafin ta na Facebook, hakan ya ci karo da sashi na 1, sakin layi na daya kuma abun hukuntawa karkashin sashi na 1, sakin layi na uku na laifukan damfara da laifuka makamantan hakan na 2006.

Terere: Yadda Bishop Oyedepo ya bude kamfani a kasar waje da sunan matarsa da 'ya'yansa

A wani labari na daban, shugaban cocin Living Faith Worldwide wanda aka fi sani da Winners Chapel International, Bishop David Oyedepo, an bayyana shi daga cikin 'yan Najeriya da suka kafa kamfanoni a tsibirin Turai na Virgin.

Kara karanta wannan

Dan majalisa ga FG: Makuden kudi kafintoci da direbobi ke samu, a wajabta musu haraji

Premium Times ta ruwaito cewa, sunan Oyedepo ya bayyana a cikin takardun Pandora wanda kungiyar 'yan jarida ta International Consortium of Investigative Journalists (ICIJ) suka jagoranta.

Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Peter Obi, Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu da na jihar Osun duk sun bayyana a cikin 'yan siyasan da suka washe kudin kasa suka adana a Turai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng